Gwamna Fubara Ya Yi Zazzafan Martani ga 'Yan Majalisa kan Yunkurin Tsige Shi

Gwamna Fubara Ya Yi Zazzafan Martani ga 'Yan Majalisa kan Yunkurin Tsige Shi

  • Gwamnatin Rivers ta ce babu wata takardar tuhume-tuhume da aka aika wa Simi Fubara daga majalisar dokokin jihar
  • Shugaban majalisar ya ce an aika wa Fubara da mataimakiyarsa sanarwa bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya
  • Biyo bayan takaddamar, lauyoyi sun gargadi majalisar kan hadarin keta doka yayin da suke kokarin tsige gwamnan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Gwamnatin jihar Rivers ta mayar da martani kan matakin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da majalisar jihar ke kokarin aiwatarwa.

A ranar Litinin, majalisar dokokin jihar, wacce ke karkashin jagorancin Martins Amaewhule, ta ce ta aikawa Simi Fubara da takardar tuhuma bisa zargin saba doka.

Fubara
Fubara ya yi martani ga majalisar Rivers kan yunkurin tsige shi. Hoto: Sir Siminalayi Fubara|Nyesom Ezonwo Wike
Asali: Facebook

Sai dai, a cewar jaridar The Punch, Kwamishinan Yada Labaran jihar Rivers, Joseph Johnson, ya ce babu wata wasika da aka aika wa Fubara dangane da tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Kara karanta wannan

Majalisa ta jero zunuban Gwamna, an fadi lokacin da ake hasashen zai rasa kujerarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Simi Fubara ya karyata ikirarin majalisa

Kwamishinan Yada Labarai na jihar Rivers, Barrister Joseph Johnson, ya bayyana cewa ba a tura wa Gwamna Fubara wata wasika ta tuhume-tuhume daga majalisar dokoki ba.

Joseph Johnson ya ce majalisar na kokarin hana gwamnan aiwatar da umarnin kotun koli kan rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar.

A cewar Johnson, ana ci gaba da takura wa ma’aikatan gwamnati da kuma masu karbar fansho sakamakon gaza gabatar da kasafin jihar.

Ya kuma ce gwamnan ya bi doka wajen umartar shugabannin kananan hukumomi da su mika mulki, tare da tsara sabon zaben kananan hukumomi a ranar 9 ga watan Agusta, 2025.

Tuhumar da majalisa ta yi wa gwamna Fubara

A ranar Litinin, shugaban majalisar dokokin Rivers, Martins Amaewhule, ya ce an aika da sanarwar tuhuma zuwa ofishin gwamna da mataimakiyarsa.

Martins Amaewhule ya ce an bi tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bukaci cewa dole ne a samu kashi daya bisa uku (1/3) na ‘yan majalisa kafin a fara shirin tsige gwamna.

Kara karanta wannan

Majalisa ta dauki matakin farko na tsige gwamna Fubara, ta jero tuhume tuhume

Amaewhule ya bukaci Gwamna Fubara da mataimakiyarsa su mayar da martani cikin kwanaki 14 kan tuhume-tuhumen da ake yi musu.

Daga cikin zarge-zargen akwai kashe kudin gwamnati ba bisa ka’ida ba da kuma nada mukarraban gwamnati ba tare da tantance su ba.

An gargadi majalisa kan tsige Fubara

Daily Trust ta wallafa cewa babban lauya Abeni Mohammed (SAN) ya gargadi majalisar dokokin Rivers da cewa dole ne a bi ka’ida kafin a iya tsige gwamna.

Ya ce dole ne a tuntuɓi Babban Alkalin Jihar don kafa kwamitin bincike da zai tantance tuhume-tuhumen da aka yi wa gwamnan.

Mohammed ya kuma ce Fubara ba zai zura ido kawai ba, ya na da damar garzayawa kotu don dakatar da yunkurin tsige shi.

Fubara
Fubara da sufeton 'yan sandan Najeriya. Hoto: Sir Siminalayi Fubara|Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Lauyan ya ce:

"Idan har majalisa ta keta dokar kasa wajen kokarin tsige gwamnan, tabbas lauyoyinsa za su san matakin da ya dace su dauka."

Kara karanta wannan

Mene ake kitsawa?: Barau ya gana da Baffa Bichi da tsohon kwamishinan Abba

Ba a kona gidan Wike a Rivers ba - Rahoto

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni na nuni da cewa ba a kona gidan ministan Abuja, Nyesom Wike da ke jihar Rivers ba.

An yada rade radin cewa an kona gidan Wike ne saboda rikicin siyasa da ya kara kamari a jihar bayan fara maganar tsige Simi Fubara gadan gadan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng