Rashawa: Obasanjo Ya Nemi Kwacewa Buhari Zani a Kasuwa, Malami Ya Kare Kansa

Rashawa: Obasanjo Ya Nemi Kwacewa Buhari Zani a Kasuwa, Malami Ya Kare Kansa

  • Tsohon Antoni Janar, Abubakar Malami SAN ya ce afuwar shugaban kasa abu ne da ke bin tsarin doka, ba shi da hannu a ciki kai tsaye
  • Malami ya karyata zargin Obasanjo na cewa yana da hannu wajen yin afuwa ga tsofaffin gwamnoni da aka kama da rashawa a kotu
  • A karkashin haka, tsohon ministan shari’ar ya bukaci a rika jefa zargi da kwakkwaran hujja ba wai kawai a fadi abu ba dalili ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya nesanta kansa daga zargin da tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi a sabon littafinsa.

Obasanjo ya yi ikirarin cewa cin hanci ya yi kamari a lokacin mulkin Muhammadu Buhari, inda ya ce Malami ne ya taka rawa wajen ba da kariya ga cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya hada Buhari da Tinubu, ya yi musu rubdugu a sabon littafinsa

Malami
Malami ya kare kansa kan zargin rashawa a lokacin Buhari. Hoto: Buhari Sallau|Bukola Saraki
Asali: Facebook

A wata hira da ya yi da jaridar Punch, Malami ya bayyana cewa afuwar shugaban kasa ga masu laifi na bisa tsarin doka kuma akwai kwamitin da ke kula da hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin da Obasanjo ya yi a kan Buhari

A cikin sabon littafinsa mai taken Nigeria: Past and Future, Obasanjo ya ce gwamnatin Buhari ta rusa kokarin yaki da cin hanci da rashawa.

Obasanjo ya ambaci yin afuwa ga tsofaffin gwamnoni biyu—Joshua Dariye na Filato da Jolly Nyame na Taraba—wanda a baya kotu ta yanke wa hukunci saboda satar kudin gwamnati.

Dariye ya fuskanci hukuncin dauri na shekaru 10 bisa wawure N1.126bn daga asusun jihar Filato, yayin da Nyame ya samu hukuncin dauri na shekaru 12 kan satar N1.64bn a jihar Taraba.

A shekarar 2022, kwamitin majalisar zartarwa karkashin jagorancin Buhari ya musu afuwa ga tsofaffin gwamnonin bisa dalilin tsufa da matsalar lafiya.

Kara karanta wannan

'Ku tsige shi': Minista ya bukaci majalisa su tuge yaronsa daga kujerar gwamna

Obasanjo
Tsohon shugaban kasa, Obasanjo. Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

A karkashin haka Obasanjo ya samu damar zargin cewa an yi hakan ne saboda karfafa cin hanci da rashawa.

Martanin Malami kan zargin Obasanjo

Malami ya ce aikinsa na Antoni Janar kawai shi ne miƙa rahoton kwamitin bada afuwa ga Shugaban Kasa da Majalisar Zartarwa, ba wai yanke shawara ba.

Ya ce:

“Yin afuwa na tafiya ne bisa tsarin doka da kundin tsarin mulki. Ba aikin Antoni Janar ba ne, kwamitin da aka kafa domin wannan aiki ne ke da alhakin yanke hukunci.”

Malami ya nuna damuwarsa kan yadda ake yawaita zarge-zargen cin hanci da rashawa ba tare da wata kwakkwarar hujja ba, yana mai cewa hakan yana rage ingancin siyasa da shugabanci.

“Dole ne idan ana zargin wani da cin hanci, a fitar da cikakkun bayanai—wa ya bayar? Nawa aka bayar? Ta wacce hanya aka bayar?

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana bayan APC ta yi barazanar tsige gwamnan PDP

"Ya kamata a sami cikakkun bayanai kafin a yi irin wadannan zarge-zargen,”

Kiran Malami ga jama’a da gwamnati

Tsohon Ministan Shari’a ya bukaci ‘yan Najeriya da su guji yarda da zarge-zarge ba tare da kwakkwaran hujja ba.

Ya ce dole ne a yi bincike mai zurfi da tabbatar da gaskiyar lamari kafin a yanke hukunci kan wani batu.

Haka kuma ya bukaci shugabanni da ‘yan siyasa su daina yin zarge-zarge marasa tushe domin bata sunan wasu.

Obasanjo ya zargi Tinubu ta rashawa

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da karfafa rashawa.

Obasanjo ya ce hanyar Legas zuwa Kalaba da sabon ofishin mataimakin shugaban kasa da aka yi a gwamnatin Bola Tinubu kashe kudi ne ba ta hanyar da ta dace ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng