Sauki na Karuwa: Farashin Litar Man Fetur Ya Kara Sauka a Najeriya
- Bayanai na nuni da cewa farashin shigo da kowace litar man fetur ya sauka zuwa N797.66, bisa sababbin alkaluma
- Sai dai 'yan kasuwar mai sun ce yawan raguwar farashin yana jawo musu hasarar kimanin fiye da N2bn a kullum
- Hakan na zuwa ne bayan matatar Dangote ta rage farashin litar fetur daga N825 zuwa N815 a makon da ya wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rahotanni sun nuna cewa farashin shigo da litar man fetur ya fadi zuwa N797.66 a ranar Litinin.
Sai dai duka da haka, ‘yan kasuwar mai sun bayyana cewa suna fuskantar asara sakamakon sauyin farashin.

Asali: Getty Images
A cewar jaridar The Punch, ‘yan kasuwar sun ce raguwar farashin na haddasa musu matsala, domin kuwa a halin yanzu suna tafka asarar kimanin N2.5bn a kowace rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bugu da kari, wasu ‘yan kasuwa sun bukaci a kafa doka da za ta hana sauya farashin mai a kasuwa sai bayan wata shida, amma har yanzu ba a tabbatar da amincewa da wannan bukata ba.
Tasirin sauke farashin man Dangote
Sabon rahoton da aka fitar ya nuna cewa farashin lodin mai daga matatar Dangote ya ragu daga N825 zuwa N815 a makon da ya gabata.
Wannan mataki ya sa gidajen ajiye mai masu zaman kansu suka sauke farashinsu domin gujewa rasa abokan ciniki.
Masana sun bayyana cewa wannan sauyi na haddasa hasara ga masu shigo da mai, inda ake kiyasta suna tafka asarar N75bn a kowanne wata.
'Yan kasuwan fetur na fama da asara
A cewar mataimakin shugaban kungiyar masu sayar da mai ta kasa (IPMAN), Hammed Fashola, raguwar farashin mai na kara rikidar da kasuwanci, duk da cewa ya amfani ‘yan Najeriya.
Ya ce:
“Wannan matsalar na hana masu sayar da mai samun riba, saboda haka da dama daga cikinsu na rage yawan man da suke saya don kaucewa karin hasara.”
Haka zalika, rahoton ya nuna cewa farashin man fetur da ake shigowa da shi a Najeriya ya ragu daga N817.82 zuwa N797.66 cikin mako daya.
Raguwar farashi na nuna yadda yanayin kasuwar man fetur ke sauyawa a cikin kankanin lokaci, abin da ke kara jefa ‘yan kasuwa cikin damuwa.
Shin dagulewar farashi zai yi tasiri?
Binciken da aka fitar ya bayyana cewa ana iya samun rikici tsakanin kamfanin mai na NNPC, matatar Dangote da masu gidajen mai masu zaman kansu kan sabon tsarin farashi.
A halin yanzu, farashin man fetur a wuraren sayarwa na NPSC-NOJ ya sauka daga N817.90 zuwa N797.73, yayin da matsakaicin farashin mai a kwanaki 30 ya ragu zuwa N851.76 daga N854.15.
Haka zalika, rahoton ya nuna cewa farashin danyen mai a kasuwar duniya yana kan $70.58 kowace ganga, daga $69.88 a makon da ya gabata, yayin da darajar Dala ke kan N1,517.93.
‘Yan kasuwa sun ce akwai bukatar a duba yadda sauyin kasuwar duniya da yanayin tattalin arziki ke shafar farashin man fetur a cikin gida, Najeriya.

Asali: Twitter
Najeriya ta fi Saudiya kashe kudin hako mai
Sai dai, duk da saukin da ake samu a kwanan nan, Najeriya ta koka kan yadda ta ke kashe kudi masu yawa wajen hako danyen mai a kasar.
Wannan na zuwa ne a cikin wani rahoton da aka tattara, inda aka yi nuni da cewa, Saudiya ta fi samun sauki wajen hako danyen mai idan aka kwatanta kudin da ake kashewa.
Rahoton ya yi tsokaci da cewa, Najeriya na biyan kusan ninkin abin da Saudiyya ke kashewa a wannan babban aiki na samar da makamashi.
Hukumomi sun bayyana kukan cewa, wannan bambanci da ake da shi da kasa kamar Saudiyya zai iya shafar farashin mai a kasuwar duniya.
Nijar ta shiga matsalar man fetur
A wani rahoton, kun ji cewa Nijar ta shiga matsalar man fetur sakamakon karancin mai da ake fama da shi a kasar.
Rahotanni sun nuna cewa rashin jituwa da aka samu tsakin kasar da wani kamfanin mai na China na cikin abin da ya jefa Nijar a matsalar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Salisu Ibrahim ya fadada wannan labarin ta hanyar ba da bayani kan yadda Najeriya ke rasa kudade wajen hako mai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng