'Yan Bindiga Sun Farmaki 'Yan Kasuwa a Ƙatsina, Sun Hallaka Bayin Allah
- Ƴan bindiga sun yi ta'asa a jihar Katsina bayan sun farmaki wasu ƴan kasuwa da suka fita neman na sanyawa a bakin salati
- Miyagun ƴan bindigan sun hallaka ƴan kasuwa 12 da suka fito daga Ƙaduna, waɗanda ke sana'ar tumatur a ƙaramar hukumar Faskari
- Tsagerun sun kuma yi garkuwa da wasu ƴan kasuwa guda biyar zuwa cikin daji bayan sun harbi tayoyin motar da ke ɗauke da su
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Ƴan bindigan ɗauke da makamai sun hallaka wasu ƴan kasuwa 12 a jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun hallaka ƴan kasuwa masu sana'ar tumatur a kasuwar Danmagaji da ke Zaria, a jihar Kaduna, bayan sun kai musu hari.

Asali: Twitter
Ƴan kasuwa sun gamu da ajalinsu a Katsina
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kuma sace mutum huɗu daga cikinsu a yayin harin da suka kai musu hari a jihar Katsina.

Kara karanta wannan
Janar Tsiga: Yadda 'yan bindiga suka shammaci jama'a, suka sace tsohon shugaban NYSC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan kasuwar dai sun tafi jihohin Katsina da Zamfara ne domin siyen tumatur lokacin da lamarin ya ritsa da su.
Ƴan bindigan dai sun yi musu kwanton ɓauna a hanyarsu ta dawowa a kusa da garin Tafoki, da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Yadda ƴan bindiga suka kashe ƴan kasuwan
Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigan sun harbi tayoyin motar da ke ɗauke da ƴan kasuwan ne lokacin da take tsaka da tafiya, wanda hakan ya sanya ta faɗa cikin rami.
Wani mazaunin garin Tafoki ya bayyana cewa lamarin ya auku ne kusan kwanaki huɗu da suka wuce.
"Lamarin ya faru kusan kwana huɗu zuwa biyar da suka wuce. Da farko, an gano gawarwaki biyar a daren ranar da abin ya faru. Amma washegari, an tono gawarwaki bakwai da suka maƙale a ƙarƙashin kayayyakinsu."
"Ƴan bindigan sun kuma sace ƴan kasuwa biyar amma daga baya ɗaya daga cikinsu ya tsere."
- Wata majiya
Ƴan bindiga sun kashe ɗan kasuwa
A wani harin na daban, an ji cewa ƴan bindiga sun buɗe wuta kan wasu ƴan kasuwa da ke tafiya a hanyar Dandume.
Ƴan bindigan a yayin harin, sun hallaka wani wani shahararren ɗan kasuwa a ranar Litinin, 10 ga watan Fabrairun 2025.
Mutane sun damu kan yawaitar hare-hare
Mazauna yankin sun nuna damuwa kan yadda hare-hare ke ƙaruwa a yankin Funtua da kewaye.
Sun danganta ƙaruwar samun hare-haren na ƴan bindiga da sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla a jihar Kaduna.
Ƴan bindiga sun ajiye makamansu a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu shahararrun ƴan bindiga da suka addabi mutane a jihar Katsina, sun rungumi zaman lafiya tare da ajiye makamansu.
Shahararrun ƴan bindigan sun yi ƙaurin suna wajen addabar mutanen ƙananan hukumomin Jibia, Safana da Batsari na jihar Katsina.
Tubabbbun ƴan bindigan sun kuma sako mutanen da suka yi garkuwa da su, inda suka yi kira ga gwamnati da ta samar musu da ababen more rayuwa a yankunansu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng