Nasara ta samu: Rundunar ƴan sanda ta yi holen manyan ƴan fashi 4 a Katsina

Nasara ta samu: Rundunar ƴan sanda ta yi holen manyan ƴan fashi 4 a Katsina

- Yan sandan jihar Katsina sun gurfanar da wasu kasurguman yan bindiga

- Har ila yau rundunar yan sandan ta baje kolin wani dillalin dalar Amurka na bogi

- An yi nasarar cafke miyagun ne bayan samun wasu muhimman bayanai na sirri

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta gurfanar da wasu bindiga biyu da ta kama, masu fashi da makami da wani dillalin dalar Amurka na bogi a Katsina.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Gambo Isa ya fada ma manema labarai cewa an kama manyan yan fashin biyu masu suna: Idi Sabi’u Dila, 30, da dayan da ba’a san sunansa ba.

An kama su ne a kauyen Mununu, karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, bayan an samu bayanai abun dogaro, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Saboda gaza ɗaukar ɗawainiya: Kotu ta warware auren shekaru 7

Nasara ta samu: Rundunar ƴan sanda ta yi holen manyan ƴan fashi 4 a Katsina
Nasara ta samu: Rundunar ƴan sanda ta yi holen manyan ƴan fashi 4 a Katsina Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Ya ce: “Dan bindigan ya hadu da bacin rana ne lokacin da aka kama shi a Sheme a hanyarsa ta zuwa Faskari. A yayin bincike, mai laifin ya fallasa cewa shi dan kungiyar yan bindiga ne na wani Melaya Alhaji Gandu na dajin Munhaye, karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.

“Hakazalika, mai laifin ya tona cewa da shi aka kai hare-hare a kauyen Kadisau, karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina a ranar 9 ga watan Yulin 2020 wanda ya yi sanadiyar kashe jama’a da dama da kuma hare-hare makamantan haka a jihohin Katsina da Zamfara."

Kakakin rundunar ya kuma gurfanar da wasu manyan yan bindiga da ke addabar kananan hukumomin Safana da Jibia.

KU KARANTA KUMA: Batanci ga Annabi: An kafa sharudda 4 a kan mika Rahama Sadau gaban kotu

Ya ce: “DPO na Batsari ya jagoranci rundunar Operation Puff Adder da Sharan Daji zuwa jejin Rugu sannan suka yi nasarar kama wani kasurgumin dan fashi, Sani Sulen Bayi wanda aka fi sani da Shaho na kauyen Manawa, karamar hukumar Batsari na jihar Katsina.

"A yayin bincike, ya tona cewa shi dan kungiyar wani Audu Maisaje da Lawo Mai Shoda ne duk a Bakin Daji, Sabon Garin Dunburawa, a yankin dajin Rugu."

An kuma gurfanar da wasu kungiyar yan fashi ciki harda wani Badamasi Ismail mai shekaru 20 na kwatas din Abatuwa, Katsina.

A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Katsina, a ranar Alhamis, ta yi holin wani matashin dan bindiga mai shekaru 30 da ake kira da Idi Dila 'sarkin wayo'.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel