Dangote ya bada tallafin N60m ga mata yan kasuwa da marasa galihu a jihar Katsina

Dangote ya bada tallafin N60m ga mata yan kasuwa da marasa galihu a jihar Katsina

Gidauniyar Dangote ta bada tallafin kudi milyan 60 domin rabawa mata yan kasuwa masu kananan jari da wasu marasa galihu a kananan hukumomin jihar Katsina shida.

Shugaban kwamitin rabar da kudin, Rayyana Lawal, ta bayyana hakan ne a ranar Laraba a garin Daura yayinda ake kaddamar da shirin nada kwamitocin kananan hukumomin da zasu amfana.

A cewar Hajiya Rayyana, kowace kwamiti na kunshe shugaba, mai anguwa, manyan limamai, sakatarorin ilin, hadimar shugaban karamar hukuma kan harkokin mata da kuma shugabar matan jam'iyyar APC.

Kananan hukumomi shida da zasu amfana da wannan tallafi sune Daura, Sandamu, Zango, Baure, Mashi da Maiadua.

Ta kara da cewa za'a baiwa kowace karamar hukuma milyan goma kuma kowanne daga cikin matan zata samu tallafin N10,000.

Rayyana Lawal ta bayyana cewa marasa aikin yi da wadanda basu samu shiga shirin N-Power ba kadai zasu amfana da tallafin.

Za'a fara rijistan wadanda zasu amfana da wannan tallafi cikin makonni biyu masu zuwa.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta bada rahoton cewa shugabannin kananan hukumomin da zasu amfana da masu anguwar garuruwan sun gana a Daura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng