'Abba ne Kaɗai Zai Iya Nada Sarki': Gwamnatin Kano Ta Roki Tinubu kan Sarauta
- Gwamnatin Kano ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya cire Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga Fadar Nasarawa
- Gwamnatin ta ce hakan zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da kowa ke bukata tun bayan rigimar sarauta
- Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ya ce matasan Kano sun gaji da halin da ake ciki, yana mai cewa dole a kiyaye dimukuradiyya
- Gwamnati ta jaddada cewa doka ce ta mayar da Muhammadu Sanusi II sarauta, don haka dole ne a mutunta dokar tare da aiwatar da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta tura bukata ta musamman ga shugaban kasa, Bola Tinubu kan rigimar sarauta.
Gwamnatin ta bukaci Bola Tinubu da ya ba da umarnin cire Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga Fadar Nasarawa.

Asali: Facebook
Rigimar sarauta: Zargin da gwamnatin Kano ke yi
Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo shi ya yi wannan roko inda ya sake jaddada matsayin gwamnati, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin ta ce hakan zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar kamar yadda aka saba.
Gwamnatin ta zargi wasu mutane da amfani da ci gaba da zaman sarkin a fadar don hura wutar rikici a fadin Kano.
Aminu Abdussalam Gwarzo ya ce:
"Muna rokon Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya cire sarkin da ya nada kuma ya ajiye a makabarta.
"Mutanen Kano, sun gaji da wannan abin, akwai mamaki yadda ake harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zanga cikin lumana, har ma ana zargin amfani da harsasai.
"Da yamma, motocin sojoji sun rika zagayawa, har ma suka tsaya a gabana, amma ba za mu bari a razana mu ba.
"Wannan dimukuradiyya ce, kuma dole a kiyaye ta da muna goyon bayan matasan da suka fito don bayyana damuwarsu."

Asali: Twitter
Gwamnatin Kano ta fadi sahihin Sarki a jihar
Gwarzo ya ce:
"Kano tuni ta nada sarki, kuma shi ne Muhammadu Sanusi II. Yau, ko da kai 'Sarkin Duniya' ne, ba za ka iya nada sarki a Kano ba sai Gwamna Abba Kabir Yusuf."
Gwarzo ya kara da cewa ci gaba da zaman Aminu Ado Bayero a Fadar Nasarawa wata dabara ce ta hana Gwamnatin Kano yin aikinta yadda ya kamata.
Ya ce zanga-zangar da mutanen Kano suka yi hakki ne da ke cikin dimukuradiyya, kuma gwamnati ba za ta yarda a tauye 'yancin su ba, cewar The Guardian.
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa doka ce ta mayar da Muhammadu Sanusi II Sarki, kuma dole ne a mutunta wannan doka tare da aiwatar da ita.
Jami'an tsaro sun kange hanyar fadar Nasarawa
Kun ji cewa ƴan sanda da sauran jami'an tsaro sun tsaurara matakan tsaro a titin zuwa fadar Nasarawa, wurin da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yake zaune.
Majiyoyi sun nuna cewa jami'an tsaron sun toshe dukkan hanyoyin da ke kai wa zuwa ƙaramar fadar saboda zargin ta da husuma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng