'Asara ce': Dillalan Mai Sun Koka kan Rage Farashin Fetur, Sun Kawo Mafita Mai Ɗorewa
- Kungiyar PETROAN ta soki saukar farashin man fetur a kai a kai, tana cewa 'yan kasuwa na ci gaba da fuskantar asara mai yawa
- PETROAN ta nemi a kafa doka da za ta kayyade sauya farashi zuwa sau daya a watanni shida domin hana rashin tabbas a kasuwa
- Kungiyar ta marawa shigo da man fetur baya, ta ce hakan zai kawo karshen danniya daga kamfani daya da ya mamaye kasuwa gaba daya
- Ta bukaci hadin gwiwar hukumomi da 'yan kasuwa don kafa tsarin da zai tabbatar da farashi mai dorewa da kare masu amfani da kayayyaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Kungiyar masu sayar da man fetur a Najeriya (PETROAN) ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda ake ci gaba da rage farashin fetur.

Kara karanta wannan
Ramadan: Direba ya murkushe sufetan ɗan sanda da ke bakin aiki a masallacin Abuja
Kungiyar ta ce 'yan kasuwa na ci gaba da fuskantar asara, ta ce akwai bukatar a kafa doka da za ta tabbatar da cewa ba za a sauya farashi ba sai bayan watanni shida.

Asali: UGC
PETROAN ta bukaci kawo sauyin farashin fetur
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na PETROAN, Joseph Obele ya fitar, Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar PETROAN ta canza matsayinta, ta ce ya kamata a karfafa shigo da fetur don dakile danniya.
Game da daidaiton farashi, kungiyar ta bayyana cewa hauhawar farashin fetur yana iya shafar kudin sufuri, abinci da ma rayuwar yau da kullum.
Sanarwar ta ce:
"Rage farashin da aka yi kwatsam ya haddasa babbar asara, inda 'yan kasuwa ke lissafin asarar su a biliyoyin naira."

Asali: Getty Images
Kungiyar PETROAN ta kawo mafita kan haka
Haka kuma, sauyin farashin yana barazana ga cigaban kasuwancin man fetur, wanda zai iya kaiwa ga rage ma’aikata da tabarbarewar tattalin arziki.
Domin magance wadannan matsaloli, PETROAN ta bukaci a kafa doka da za ta tabbatar da farashi mai dorewa na akalla watanni shida, cewar The Guardian.
PETROAN ta ce hakan zai taimaka wajen rage rashin tabbas da hadarin saka jari a harkar man fetur, tare da kare masu amfani da kayayyaki.
Yayin da yake bayani, Obele ya ce bangaren man fetur na fuskantar matsaloli irinsu hauhawar farashi, danniya a kasuwa da kuma rashin gasa mai kyau.
Ya ce:
"Bayan tuntuba da manyan masu ruwa da tsaki, PETROAN ta yanke shawarar kare gasa mai tsafta da dakile hauhawar farashi."
Domin cimma wannan, kungiyar ta bukaci a bude hanyoyi daban-daban na samar da fetur daga matatun Dangote, NNPCL, da shigo da kaya daga waje.
PETROAN ta bukaci gwamnati ta cire shinge ga sababbin masu kasuwanci, da hana kamfani daya mamaye kasuwa gaba daya.
Ana hasashen fetur zai sake tsada
Kun ji cewa an ruwaito cewa kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya dakatar da sayar da ɗanyen man fetur a Naira ga matatun man cikin gida.
Wannan matakin da kamfanin NNPCL ya ɗauka zai iya sanyawa matatun mai su riƙa samun ɗanyen man fetur da tsada da ka iya kara farashin mai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng