Za a Koma Gidan Jiya: NNPCL Ya Dauki Matakin da Zai Sa Fetur Ya Yi Tsada

Za a Koma Gidan Jiya: NNPCL Ya Dauki Matakin da Zai Sa Fetur Ya Yi Tsada

  • Sabuwar barazana ta kunno kai kan sauƙin farashin litar man fetur da aka samu cikin ƴan kwanakin nan a Najeriya
  • Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya dakatar da sayar da ɗanyen man fetur a Naira ga matatun man cikin gida
  • Wannan matakin da kamfanin NNPCL ya ɗauka zai iya sanyawa matatun mai su riƙa samun ɗanyen man fetur da tsada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya kawo cikas ga yarjejeniyar sayar da ɗanyen man fetur ga matatun cikin gida, ciki har da matatar Dangote.

Kamfanin NNPCL ya dakatar da yarjejeniyar ba da ɗanyen mai a kan kuɗin Naira ga matatun man Najeriya.

NNPCL ya daina sayar da danyen fetur a Naira
NNPCL ya dakatar da sayar da danyen fetur a Naira ga matatun Najeriya Hoto: @nnpclimited
Asali: Twitter

Jaridar TheCable ta rahoto cewa wasu majiyoyi ne suka sanar da ita hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ci gaban na iya haddasa ƙarin farashin fetur a matatun mai na cikin gida, ciki har da ta Dangote da ke garin Legas.

Kara karanta wannan

Farashin man fetur ya kama hanyar ƙara araha, sauƙi zai lulluɓe ƴan Najeriya

Yanzu haka matatun nan za su dogara ne kacokan ga masu samar da ɗanyen mai daga ƙasashen waje.

Meyasa NNPCL ya dakatar da tsarin?

Rahotanni sun bayyana cewa NNPCL ya sanar da matatun cewa ya riga ya sayar da ɗanyen man da zai samar a nan gaba, duk da cewa yawan ɗanyen man da ake haƙowa yanzu ya fi na lokacin da yarjejeniyar ta fara aiki.

A hukumance, Najeriya ta fara sayar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida ta hanyar amfani da Naira a ranar 1 ga watan Oktoba, 2024.

Sai dai majiyoyi daban-daban sun tabbatar da cewa an dakatar da wannan tsari har zuwa shekarar 2030.

Wata majiya mai ƙarfi ta tabbatar da cewa NNPCL ya sanar da matatar Dangote da sauran matatun cikin gida cewa ba za ta ƙara basu ɗanyen mai ba, saboda ta riga ta sayar da duk ɗanyen man da za ta samar har zuwa 2030.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta kare matakin kulle makarantu a Ramadan, ta tura sako ga CAN

"Duk da ƙoƙarin ƙarfafa ƙarfin tace mai a cikin gida, Najeriya ta kashe sama da dala biliyan 4.3 wajen shigo da lita biliyan 6.38 na fetur da dizil cikin watanni biyar kacal."

- Wata majiya

Kamfanin NNPCL na shigo da fetur daga waje

An bayyana cewa kamfanin NNPCL na ɗaya daga cikin kamfanonin da har yanzu ke shigo da kayayyakin mai daga ƙasashen waje.

Wata majiya ta ce a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke fatan rage farashin man fetur, NNPCL ya yanke shawarar dakatar da tsarin sayar da ɗanyen mai a Naira ba tare da tuntuɓar kowa ba.

Duk da cewa matatar Dangote ta ƙi yin tsokaci kan wannan matakin na NNPCL, wani jami’in kamfanin ya bayyana cewa za su yi nazari a kan zaɓin da suke da shi kafin ɗaukar matakin da ya dace.

NNPCL ya rage farashin man fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), ya rage farashin litar man fetur a gidajen man da ke ƙarƙashinsa.

Kara karanta wannan

Abin da dillalai suka hango bayan NNPCL da matatar Ɗangote sun rage farashin fetur

Kamfanin NNPCL ya ɗauki matakin ne bayan matatar Dangote ta sanar da rage farashin fetur da take siyarwa ƴan kasuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng