Babban Farfesa a Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Fadi Ana Azumi, Ya Mutu a Hanyar Asibiti
- Jami’ar Obafemi Awolowo ta shiga jimami bayan rasuwar Farfesa Jimoh Olanipekun, wanda ya yanke jiki ya fadi ana tsakiyar taro
- An gaggauta kai shi asibitin jami’ar, amma daga bisani aka mayar da shi babban asibitin koyarwa, a nan likitoci suka tabbatar da rasuwarsa
- Shugaban jami’ar, Farfesa Adebayo Bamire, ya jajantawa iyalansa, yana mai cewa jami’ar za ta ci gaba da tunawa da gudunmawar marigayin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Ile-Ife, a jihar Osun, ta shiga jimami bayan wani fitaccen Farfesa, Jimoh Olanipekun, ya rasu a lokacin da ake wani taro na jami'ar.
A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Abiodun Olarewaju, ya fitar, farfesan ya kamu da rashin lafiyar farat daya a yayin taron sashe-sashe na jami'ar a ranar Laraba, 5 ga watan Maris, 2025.

Asali: Twitter
Farfesan jami'ar OAU ya mutu a hanyar asibiti
Olarewaju ya bayyana cewa, yayin da taron ke gudana, wasu daga cikin abokan aikin Farfesa Jimoh sun lura da yadda numfashinsa ya canza, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce, ganin malamin ya yanke jiki ya fadi, ya sa aka hanzarta kai shi cibiyar kiwon lafiya da kula da marasa lafiya ta Jami’ar.
Bayan gudanar da binciken lafiyarsa cikin gaggawa, tawagar likitocin da ke bakin aiki sun bayar da shawarar a wuce da shi zuwa babban asibitin koyarwa na jami’ar Obafemi Awolowo (OAUTHC), wanda shi ma ya ke a garin Ile-Ife.
A can ne likitoci suka tabbatar da cewa Farfesa Jimoh Olanipekun ya rasu, lamarin da ya jefa al’ummar jami’ar cikin alhini da jimami.
Mutuwar farfesan ta girgiza jami'ar OAU
Shugaban jami’ar OAU, Farfesa Adebayo Bamire, ya jagoranci wasu daga cikin shugabannin jami’ar zuwa gidan marigayin domin jajanta wa iyalansa.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya
Bamire ya bayyana cewa, mutuwar Farfesa Olanipekun ta farat daya ta matukar girgiza jami'ar, kasancewarsa masanin ilimi mai hazaka da jajircewa a bangaren aikinsa.
Ya karfafa wa iyalansa gwiwa da su dauki rasuwar a matsayin kaddara, yana mai tunatar da su cewa marigayin ya rayu ne da manufar kyautata rayuwar wasu.
Jami'ar ta jajantawa iyalan farfesan da ya mutu

Asali: Twitter
A cewarsa, kamar yadda littattafan addinai suka bayyana, Allah ne ke sanyawa dan Adam rai kuma shi ne ke karbewa a duk lokacin da ya ga dama.
Punch ta rahoto shugaban jami’ar ya kuma yi addu’a cewa Allah ya bai wa iyalan marigayin, sashen Falsafa, da gaba ɗaya al’ummar jami’ar hakurin jure wannan babban rashi.
Hakazalika, ya jaddada cewa jami’ar za ta ci gaba da tuna da irin gudunmawar da marigayin ya bayar wajen ci gaban ilimi da nazari.
Ya bukaci al’ummar jami’ar da su jajirce a ayyukansu tare da daukar darasi daga irin salon rayuwar Farfesa Olanipekun wanda ya sadaukar da kansa don ci-gaban ilimi.
Farfesa mai lalurar gani ya rigamu gidan gaskiya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an shiga jimami a jami'ar Bayero da ke Kano bayan rasuwar Farfesa mai matsalar gani na farko a Najeriya, Farfesa Jibril Isa Diso.
An rahoto cewa daliban jami'ar musamman wadanda Farfesa Jibril ya koyar da su sun shiga jimami, tare da tuna malamin a matsayin gogagge wajen koyarwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng