Wani rikakken Farfesa a Jami'ar ABU Zaria ya rasu kwatsam

Wani rikakken Farfesa a Jami'ar ABU Zaria ya rasu kwatsam

- Wani fitaccen Malamin Kimiyya Zakari Yusuf Ibrahim ya rasu

- Babban Malamin na Jami'ar Katsina ya rasu ne a jiya da rana

- Zakari yayi fice musamman a ABU wajen sababbin shiga Jami’a

Babbar Jami'ar nan ta Ahmadu Bello da ke Zariya tayi rashin wani Bajimin Malamin ta mai suna Zakari Yusuf Ibrahim a jiya bayan yayi 'yar gajeruwar jinya. Zakari ya dauki dogon lokaci yana koyarwa a Jami'ar ABU da ke Arewacin kasar.

Wani rikakken Farfesa a Jami'ar ABU Zaria ya rasu kwatsam

Dr. Zakari Yusuf na Jami'ar ABU ya bar Duniya

Dr. Zakari Yusuf Ibrahim wanda shi ne Shugaban bangaren kimiyya na Physics ya rasu ne a jiya bayan da ya fadi da rana lokacin da ya gama wani darasi. Babban Malamin ya kan koyar dama a Jami'ar Ummaru Musa Yaradua ta Katsina.

KU KARANTA: Ana iya ganin Shehunnai ko da sun bar Duniya?

Kwastam bayan babban Malamin ya kammala bada darasi ne sai ya fadi. Daga nan kuma ya shiga gargara har Allah yayi masa cikawa. Abin mamaki shi ne a jiya ne Jami'ar Ahmadu Bello ta tabbatar da shi a matsayin Farfesa.

Zakari har zuwa lokacin da ya rasu shi ne Shugaban sashen Physics. Hazikin Malamin yayi Digiri na daya da na biyu ne a bangaren ya kuma yi Digirin sa na uku na PhD a fannin Nukiliya. Malamin yayi fice wajen 'yan aji daya a Jami'ar ABU.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel