Yan Bindiga Sun Kutsa Wurin Ibadan, Sun Yi Garkuwa da Babban Limami da Ɗalibi
- Ƴan bindiga sun kai hari cocin Katolika a ƙaramar hukumar Etsako ta Gabas a jihar Edo, sun sace limami da ɗalibinsa
- Rundunar ƴan sanda reshen jihar Edo ta tabbatar da kai harin, ta ce dakarunta sun kashe ɗan bindiga ɗaya, sun kama mutane
- Kwamishinar ƴan sandan Edo ta tura dakarun ƴan sanda na sashen yaƙi da masu garkuwa da mutane domin ceto mutanen
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Wasu tsagerun ƴan bindiga sun kai farmaki cocin katolika da ke yankin ƙaramar hukumar Etsako ta Gabas a jihar Edo.
‘Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Limamin Katolika, Rabaran Philip Ekeli, da wani dalibin addini, Peter Andrew.

Asali: Original
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Edo ta tabbatar da afkuwar lamarin, tana mai cewa dakarunta sun kashe ɗaya daga cikin maharan, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan sanda sun kai ɗauki da wuri
Dakarun ƴan sandan sun kuma cafke ƙarin mutum huɗu daga cikin masu garkuwa da mutanen yayin da binciken ceto limamin ya kankama.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na dare a ranar Litinin, a Cocin Katolika mai suna St. Peter da ke Ivukwa, karamar hukumar Etsako ta Gabas.
Yadda ƴan bindiga suka kutsa cocin
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun afka wa cocin suna harbi, sannan suka yi awon gaba da limamin da dalibinsa zuwa daji.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ‘yan sandan jihar, Moses Yamu, ya ce sun samu rahoton abin da ya faru kuma nan take aka tura dakaru domin su kai ɗauki.
Ya ce rundunar ƴan sandan ta hada gwiwa da kungiyoyin ƴan sa-kai da mafarauta, suka tunkari maharan aka yi ɗauki ba daɗi.
An kama mutum 4 da hannu a harin

Kara karanta wannan
Ramadan: Ɗan Shugaba Bola Tinubu ya yamutsa siyasar Kano a wurin buɗa bakin azumi
Moses Yamu ya ce an kama mutane hudu da ake zargin suna da hannu a garkuwar, wadanda suka hada da Murtala Ibrahim (32), Joshua Joseph (31), Sadiq Sheidu (35), da Sunday Bulus (28).
Abubuwan da aka kwato daga hannun su sun hada da takalman roba guda biyu, waya kirar Tecno mai layuka biyu, da kuma na'urar caji (power bank).

Asali: Twitter
Sauran kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da rigar da ke da alamar makami, jaka dauke da biski da shayin Nescafé, da kuma kudi har N168,850 a cewar rahoton Vanguard.
Kwamishinar ‘yan sanda ta jihar Edo, Betty Otimenyin, ta tura jami’an sashen yaki da garkuwa da mutane domin su hada kai da rundunar soji da sauran jami’ai a yankin.
Ta nemi wannan haɗin guiwar dakarun tsaron ne domin tabbatar da kubutar da wadanda aka sace ba tare da wani sharadi ba, da kuma cafke sauran masu laifin.
Ƴan bindiga sun ɗauki mataimakin ciyaman
A wani labarin, kun ji cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Bukkuyum, Bala Muhammad, tare da wasu fasinjoji a titin Gusau.
An tattaro cewa mahara sun sace Bala Muhammad tare da ma’aikatan karamar hukumar guda uku da kuma wasu fasinjoji a ranar Litinin da yamma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng