'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Kauyen Katsina, duk da Sulhun da Aka Yi da Su
- Ana cikin gudanar da azumin watan Ramadan, ƴan bindiga sun kai hari a ƙaramar hukumar Batsari da ke jihar Katsina
- Tsagerun ƴan bindigan sun hallaka mutum ɗaya a harin da suka kai a ƙauyen Madaddaban Fegi a ƙaramar hukumar
- Bayan samun rahoto, jami'an tsaro sun kai ɗauki zuwa inda lamarin ya auku, amma kafin su isa ƴan bindigan sun tsere
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun kai hari a ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Madaddaban Fegi da ke ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina a ranar Talata, 4 ga watan Maris, 2025.

Asali: Original
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka kai hari a Katsina
Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a ƙauyen, sun kashe wani mutum mai shekaru 30 kafin su tsere zuwa dajin Safana da ke kusa.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kutsa bayan garin ƙauyen da misalin ƙarfe 1:00 na rana inda suka harbe wani mutum mai suna Sanusi Iliyasu har lahira.
Da jin labarin harin, dakarun tsaro suka yi gaggawar ƙaddamar da sintiri zuwa wurin da abin ya faru. Sai dai kafin su isa, ƴan bindigan sun riga sun tsere zuwa cikin daji.
Bayan faruwar lamarin, an ɗauki gawar mamacin zuwa babban asibitin Batsari domin likita ya duba gawarsa.
Daga nan ne aka mika gawar ga iyalansa don yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Har zuwa yanzu, ba a samu wani cikakken bayani ba dangane da ko an samu nasarar kama wani daga cikin maharan ba.
Mutane sun damu da hare-haren ƴan bindiga
Mutanen yankin dai sun bayyana damuwarsu kan yawaitar hare-haren ƴan bindiga a ƙauyukan su, inda suka yi kira ga hukumomi da su ƙara matakan tsaro don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
A ƴan watannin da suka gabata, yankunan Batsari, Safana, da Jibia sun fuskanci hare-hare daga ƴan bindiga.
Wannan lamari dai ya jefa al’ummar wurin cikin fargaba da tsoron fita domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Duk da kokarin da jami’an tsaro ke yi na daƙile ayyukan ta’addanci a yankin, har yanzu akwai buƙatar ƙara yawan dakarun tsaro da kuma inganta hanyoyin tattara bayanan sirri don hana kai hare-haren ƴan bindiga.
Mazauna yankin na fatan cewa gwamnati da hukumomin tsaro za su ɗauki matakai masu ƙarfi domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabe su.
Ƴan bindiga sun miƙa wuya a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa shahararren ɗan bindiga, Abu Radde tare da yaransa sun ajiye makamansu a jihar Katsina.
Tantirin ɗan bindigan tare da yaransa sun nemi sulhu inda suka saki mutane 10 da suka yi garkuwa da su, waɗanda ke tsare a hannunsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng