Gwamna Ya Fara Ruguza Gidajen da Masu Garkuwa ke Boye Mutane a cikin Gari

Gwamna Ya Fara Ruguza Gidajen da Masu Garkuwa ke Boye Mutane a cikin Gari

  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Edo ta fara rushe gidajen da ake amfani da su wajen boye mutanen da aka yi garkuwa da su a jihar
  • Wasu da ake zargi da garkuwa da mutane sun amsa laifinsu tare da bayyana yadda suka karɓi N10m hannun wasu mutane da suka sace
  • Mai ba gwamnan Edo shawara kan tsaro, Akhere Paul, ya ce dokar jihar ta tanadi rusa duk wani gida da aka gano yana da alaka da ta’addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - A wani mataki na dakile garkuwa da mutane a jihar Edo, gwamnati ta fara rusa gidajen da ake amfani da su wajen boye wadanda aka sace.

Wasu da ake zargi da aikata laifin sun amsa cewa sun karɓi kudin fansa na N10m a harin su na karshe kafin su shiga hannun hukuma.

Kara karanta wannan

'Dan bindiga ya tono sirrin 'yan ta'adda ga sojoji kafin 'yan uwasa su harbe shi

Rusau
An rusa gidajen masu garkuwa a Edo. Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

A cewar jaridar Punch rusau din na gudana ne a yankunan Illeh da Uromi, inda aka gano wasu gidajen da ake amfani da su wajen aikata laifuffuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara rusa gidajen masu garkuwa a Edo

Gwamnatin Edo ta fara rushe gidajen da ake amfani da su wajen aikata laifukan garkuwa da mutane a sassan jihar.

Mai bai wa gwamnan Edo shawara kan tsaro, Akhere Paul, ya ce dokar jihar ta tanadi rusa duk wani gida da aka gano yana da alaka da ta’addanci.

Ya ce wannan mataki zai zama izina ga masu taimakawa ‘yan ta’adda tare da kare lafiyar jama’a daga ayyukan miyagun mutane.

The Nation ta wallafa cewa Akhere Paul ya ce:

“Duk wanda zai bayar da haya, ya tabbatar da yin bincike mai kyau kan wanda zai zauna a gidansa domin hana shigowar masu aikata laifuka,”

Kara karanta wannan

Dangote ya fadi wuraren da za a rika samun fetur dinsa a farashi mai rahusa

Masu garkuwa da mutane sun amsa laifinsu

Wasu mutanen da ake zargi, Utubor Uchenna da Felix Ebama, sun bayyana yadda suka gudanar da ayyukan su na garkuwa da mutane.

Sun bayyana cewa sun samu N10m daga wani mutum da suka sace tare da wata mace saboda suna tafiya da motoci masu tsada.

Uchenna ya ce:

“Mun sace wani mutum da wata mace saboda mun gansu suna tafiya da mota mai numfashi. Bayan an biya kudin fansa na N10m, mun sake su ba tare da wata illa ba.”

Ya kuma kara da cewa sun aikata irin wannan laifi a lokuta daban-daban a yankin Edo ta Tsakiya kafin su shiga hannun jami’an tsaro.

Za a cigaba da yakar masu garkuwa

Mai bai wa gwamnan Edo shawara kan tsaro, Akhere Paul, ya tabbatar da cewa za a cigaba da rusa gidajen masu laifi har sai an kawar da ‘yan ta’adda a jihar.

Kara karanta wannan

Ramadan: Hukumar Hisbah ta ci gaba da aikin Allah cikin watan Azumi a Kano

Ya ce gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya umarci jami’an tsaro da su yi aiki tukuru don ganin an magance garkuwa da mutane a jihar.

Gwamnan Edo
Gwamnan jihar Edo yana jawabi a wani taro. Hoto: Monday Okpebholo
Asali: Facebook

Shugaban rundunar musamman da ke yaki da laifuffuka a Edo, SP Michael Anetor, ya bukaci al’umma da su bayar da hadin kai wajen yaki da miyagun ayyuka.

An kashe babban dan bindiga a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an tsaro sun kashe wani kasurgumin dan bindiga da ya shahara da kashe mutane.

Rahotanni sun nuna cewa an kama dan bindigar ne a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, kuma ya bayyana irin mutanen da ya yi wa ta'addanci a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Ibrahim Yusuf, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng