Kamfanoni 8 na Neman Durkusa Kasafin 2025, Sun ki Biyan Gwamnati Bashin N9.4tn
- Rahotanni sun nuna kwamitin Majalisar Wakilai ya ba wasu kamfanonin mai takwas wa'adin sa'o'i 72 su bayyana gaban sa
- Binciken 'yan majalisar ya nuna cewa kamfanonin na dauke da bashin Naira tiriliyan 9.4 da suka kasa biyan gwamnatin tarayya
- Majalisar tarayyar ta gargadi kamfanonin cewa za a dauki matakin doka idan suka gaza bayyana a daidai lokacin da aka saka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kwamitin Majalisar Wakilai da ke bincike kan bashin Naira tiriliyan 9.4 da gwamnatatin tarayya ke bin wasu kamfanoni ya dauki matakin gaggawa.
An ruwaito cewa kwamitin ya ba kamfanoni takwas wa’adin sa’o’i 72 su gurfana a gabansa ba tare da bata lokaci ba.

Asali: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa kwamitin ya dauki wannan mataki ne bayan kamfanoni takwas daga cikin tara da aka gayyata sun ki bayyana a zaman binciken da aka gudanar a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar kwamitin, idan har kamfanonin suka ci gaba da kaucewa gayyatar da aka musu, to za a dauki matakin tilasta su biyan bashin da gwamnatin tarayya ke binsu.
Kamfanonin da majalisa ta gayyata
A yayin zaman kwamitin, kamfanin Belema Oil Producing Ltd kadai ne ya samu halartar zaman, amma an bukaci ya dawo a ranar Talata saboda jinkirin kawo takardun da ake bukata.
Sauran kamfanonin da aka gayyata amma suka ki halarta sun hada da:
- Addax Petroleum Exploration Nigeria Ltd
- AITEO Group
- All Grace Energy
- Amalgamated Oil Company Nigeria Limited
- Amni International Petroleum Development Company Limited
- Bilton Energy Limited
- Britannia-U
- Waltersmith Petroman Limited
Kwamitin ya bayyana cewa wadannan kamfanoni sun kasa biyan bashin da suka cigaba da tarawa kansu tun kafin shekarar 2021.
Bashin ya hada da kudin haraji da kuma kudin da suka rataya a kan yarjejeniyoyin hakar mai da suka sanyawa hannu.
Jimillar bashin gwamnati ke bin kamfanonin
Rahoton da Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya gabatar ga Majalisar Wakilai ya bayyana adadin bashin da ake bin kamfanonin da suka hada da:
- Bashin harajin hakar mai ya kai Dala biliyan 1.74 a karshen shekarar 2021.
- Harajin sayar da iskar gas a kasashen waje ya kai Dala miliyan 13.8.
- Bashin harajin iskar gas a gida ya kai Naira biliyan 848.2 da sauransu
Wakilin Hukumar Kula da Harkokin Hakar Mai ta Kasa (NUPRC), Balarabe Haruna, ya gabatar da cikakken bayanin yadda gwamnati ke bin kowanne daga cikin kamfanonin bashi.
Gargadin da majalisa ta yi kan bashin
Shugaban kwamitin da ke gudanar da binciken, Hon. Tunji Olawuyi, ya soki kamfanonin da suka ki bayyana, duk da cewa an aika musu da wasiku tun ranar 28 ga Janairu, 2025.
Hon. Tunji Olawuyi ya ce:

Kara karanta wannan
Gwamna ya shiga matsala, Majalisar Dokoki ta ba shi sa'o'i 48 ya bayyana a gabanta
"Mun aika musu da gayyata don su bayyana ranar 19 ga Fabrairu, amma sun ki zuwa. Haka zalika, mun wallafa a jaridu biyar cewa za su zo ranar 3 ga Fabrairu, amma ba su zo ba."
Alakar bashin da kasafin kudin 2025
Olawuyi ya ce kudin da gwamnati ke bin kamfanonin na da muhimmanci wajen aiwatar da kasafin kudin 2025 da shugaba Tinubu ya rattaba hannu a kansa.
Saboda haka, kwamitin ya yanke shawarar bai wa kamfanonin wa’adin sa’o’i 72 su gurfana don kare kansu, ko kuma su fuskanci hukunci da kuma tilasta su biya bashin cikin kwanaki bakwai.
This Day ta ruwaito dan majalisar ya ce:
"Ta yaya kuke tsammanin za mu samar da kudi ga kasafin idan kamfanonin suka ki biyan kudin a kan lokaci?"

Asali: Twitter
'Dan majalisa ya raba kayan tallafi
A wani rahoton, kun ji cewa dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Abdulmumini Jibrin Kofa ya raba kayan tallafi a mazabarsa.
Hon. Kofa ya bayyana cewa ya raba tallafin ne domin rage radadi ga mutanensa a lokacin azumi da kuma sama musu hanyar dogaro da kai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng