Tarihin Kirkirar Jihohi daga 1967 zuwa 1996 da yadda Aka Samu Gwamnoni 36 a Yau

Tarihin Kirkirar Jihohi daga 1967 zuwa 1996 da yadda Aka Samu Gwamnoni 36 a Yau

Abuja - A yau akwai jihohi 36 a Najeriya, amma abin da mutane da yawa ba su sani ba shi ne, da farko ba haka aka fara ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Sannu a hankali ne gwamnatocin tarayya su ka rika kirkirar jihohi saboda wasu dalilai, a karshe ya zama ana da gwamnoni 36.

A rahoton nan na musamman, Legit Hausa ta dauko tarihin kirkirar jihohi a kasar nan musamman da ake ta kiraye-kirayen nan.

Sojoji
Shugaban kasan lokacin Sojoji da suka kirkiro jihohi a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Yadda aka rika kirkiro jihohi a tarihi

1. 1963 - Shiyyoyi 4

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun daga lokacin da aka samu ‘yanci a 1960, ana amfani da shiyyoyi ne a Najeriya; akwai Arewa, yamma da gabas masu cin gashin kansu.

Kara karanta wannan

Baram Barama 7 da shugaban majalisar dattawa, Akpabio ya yi gaban duniya

A shekarar 1963 aka kirkiri shiyyar tsakiyar yamma lokacin da aka rika samun tashin-tashina a yankin Kudu maso yamma na Yarbawa.

2. 1967 - Jihohi 12

Bayan shekaru bakwai, sai aka yi watsi da tsarin shiyyoyin nan, gwamnatin soja karkashin Yakubu Gowon ta sa jihohi suka zama 12.

Gowon ya kirkiro jihohi wadanda su ne: Kano, Kaduna, Kwara, Legas da Ribas, ko da sai daga baya aka canza wasu sunayen ne daga baya.

3. 1976 - Jihohi 19

Bayanin da aka samu daga shafin Rulers ya nuna a 1976 sojoji su ka kirkiro Gongola, Benuwai-Filato, Borno, Imo, Neja, Sokoto da Bauchi.

A lokacin aka samu Kuros Riba, Anambra, Bendel, Ogun, Ondo, Oyo, Benuwai da Filato a karkashin jagorancin Janar Murtala Mohammed.

4. 1987 - Jihohi 21

A shekarar 1987, shekaru biyu bayan ya hambare gwamnatin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya kirkiro wasu karin jihohi a Najeriya.

Janar Ibrahim Babangida ya maida jihohi zuwa 21, aka samu: Katsina da Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

"Manyan Arewa da za su iya rarrashin masu zanga zanga," masoyin Tinubu ya fadi sunaye 2

5. 1991 - Jihohi 30

Ibrahim Babangida ya kara yawan jihohin 1991, shi ya kirkiri Abia, Adamawa, Delta, Edo, Enugu, Jigawa, Kebbi, Kogi, Taraba da Yobe.

A lokacin nan ne kuma Abuja da aka kirkiro a 1976 ta tabbata a matsayin birnin tarayya.

6. 1996 - Jihohi 26

Janar Sani Abacha ya yi wasu sauye-sauyen fasali ga tsarin kasa a lokacinsa bayan ya gaji jihohi 30 a lokacin da ya yi juyin mulkinsa.

Marigayin ya saurari korafin jama’a, ya sake kirkiro jihohi shida a 1996. A sanadiyyar haka ne ake da gwamnoni 36 yau su na mulki a jihohi.

Jerin kwabar shugaban majalisa

Godswill Akpabio ya saba yabo magana, daga baya duniya ta yi shugaban majalisar ca a kai, an tattaro irin baram-baramarsa a rahoton nan.

Shugaban majalisar ya taba subutar bakin tona cewa an rabawa Sanatoci kudi, ya taba tona asirin badakalar da ake yi a hukumar NDDC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng