Cikakken jerin sabbin jihohi 20 da majalisa ke shawarar kirkira a Najeriya
- Majalisar dattawa ta karbi rahoton koke daga yankuna daban-daban na Najeriya kan gyara kudin tsarin mulki
- A halin yanzu, an ware wasu sassa 20 da ake sa ran su zama sabbin jihohi a Najeriya nan gaba
- Legit ta kawo muku jerin jihohin da kuma in da za a rabe su su zama jihohi masu zaman kansu
Kwamitin majalisar dattawa kan sake duba kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba da shawarar a kirkiro sabbin jihohi 20.
Kwamitin ya cimma wannan matsaya ne bayan ya duba abubuwa daban-daban da suka hada da ikon gwamnatin farar hula na kirkiro jihohi.
Majiyoyi sun shaida wa jaridar The Nation cewa ana iya gudanar da zaben raba gardama a kasa da jihohi 20.
Kwamitin ya ba da shawarar ba da matsayin jiha ga FCT. An ce jerin bukatun kafa sabbin jahohi sun yi tsawo sosai. Su ne kamar haka:
- Jihar ITAI daga Akwa Ibom
- Jihar Katagum daga Bauchi
- Jihar Okura daga Kogi ta Gabas
- Jihar Adada daga Enugu
- Jihar Gurara daga Kaduna ta Kudu
- Jihar Ijebu daga Ogun
- Jihar Ibadan daga Oyo
- Jihar Tiga daga Kano
- Jihar Ghari daga Kano
- Jihar Amana daga Adamawa
- Jihar Gongola daga Adamawa
- Jihar Mambilla daga Taraba
- Jihar Savannah daga Borno
- Jihar Okun daga Kogi
- Jihar Etiti daga shiyyar kudu maso gabas
- Jihar Orashi daga Imo da Anambra
- Njaba daga jihar Imo ta yanzu ko rabewar jihar Aba daga Abia
- Jihar Anioma daga Delta
- Jihohin Torogbene da Oil River, daga jihohin Bayelsa, Delta da Ribas
- Jihar Bayajida daga sassan Katsina, Jigawa da Zamfara
Gwamnonin PDP sun magantu bayan ficewar wasu manyan jam'iyyar jiya Talata
Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta yi kira ga mambobi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da su kwantar da hankulansu kan murabus din wasu mataimaka na jam’iyya bakwai a ranar Talata.
Kungiyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da shugabanta kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya fitar a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.
Mista Tambuwal ya bukaci duk mambobin jam'iyyar da abin ya shafa da su yi wa jam'iyyar fatan zaman lafiya, domin kuwa mambobin na ci gaba da kokarin shiga cikin lamarin.
Ya bayyana cewa kungiyar ta yi nadama da bakin ciki na rigingimun da suka faru kwanan nan a PDP.
Sokoto da sauran jihohin Najeriya guda 5, da yadda sunayensu suka samo asali
A wani jerin daban, Najeriya kasa ce da ba wai kawai ta kunshi wadataccen ma'adinai da albarkatun kasa ba, ta kunshi har ma da albarkatu masu ban mamaki. A al'adun Najeriya, babu sunan da ba shi da ma'ana kama daga sunan mutum har zuwa sunan gari.
Yayin da kowa yasan Najeriya na da jihohi 36 da babban birnin tarayya, ba kowa ne yasan ma'anar sunayen dukkan jihohin ba da kuma yadda suka samo asali.
A cikin wannan rahoton, Legit ta tattaro sunayen wasu jihohi shida da kuma yadda sunayensu suka samu a tarihi.
Asali: Legit.ng