Tsohon Shugaban Hukumar NIS Ya Mutu a Otel bayan Budurwar da Suke Tare Ta Tsere
- Rundunar ‘yan sandata tabbatar da mutuwar David Parradang, tsohon shugaban hukumar NIS, a wani otal bayan ya shiga da wata mace
- An ce ya sauka a otal ɗin Joy House, ya biya N22,000 kudin kwana ɗaya, amma aka tsinci gawarsa a ɗakin washe gari da aka je duba shi
- ‘Yan sanda sun musanta jita-jitar cewa kashe shi aka yi, inda ake yin bincike don gano matar da suka shiga dakin tare da dalilin mutuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rundunar ‘yan sanda ta Abuja ta tabbatar da mutuwar tsohon shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya, David Parradang, a wani otal bayan zuwansa da wata mace.
Kakakin rundunar, Josephine Adeh, ta bayyana cewa Parradang ya sauka a otel ɗin Joy House, Area 3 Junction, a ranar 3 ga Maris, 2025, da karfe 12 na rana.

Asali: Twitter
Tsohon shugaban NIS ya mutu a dakin otel
Josephine Ade ta ce Parradang ya isa otel ɗin ne a wata mota kirar Mercedes Benz mai launin baƙi, sai ya biya N22,000 don kwana ɗaya a ɗakin da aka ba shi, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar kakakin 'yan sanda ta ce:
"Daga nan, ya bukaci ma’aikatan otel ɗin su raka wata mata zuwa ɗakinsa. Kuma matar ta bar otal ɗin misalin ƙarfe 4:00 na yamma.
"Bayan tafiyar matar, Parradang bai sake fita daga ɗakinsa ba har zuwa safiyar 4 ga Maris, lokacin da wani abokinsa soja ya nemi su gana.
"Sojan ya isa otal ɗin tare da ma’aikatan wajen, inda suka tarar da Parradang kwance a kujerarsa, babu rai a jikinsa."
An kai gawar Parradang asibiti don bincike
Josephine ta ce bayan faruwar lamarin, ‘yan sanda daga ofishin Durumi sun isa otel din don tabbatar da tsaro da tattara shaidu daga wajen.
Ta ce jami’an tsaro sun ɗauki hotuna da kuma kwashe duk wata hujja da za ta taimaka wajen binciken gano musabbabin mutuwar Parradang.
A halin yanzu, an ruwaito cewa gawar Parradang na a asibitin tarayya na Abuja, inda aka kai shi domin gudanar da binciken da ya dace.
Kakakin 'yan sandan ta ce ma’aikatan otel ɗin suna ba da haɗin kai ga jami’an tsaro yayin da ake bincike kan abubuwan da suka faru kafin mutuwarsa.
Ana farautar wanda suka shiga daki da Parradang

Asali: Twitter
Josephine Adeh ta musanta jita-jitar da ke cewa an sace Parradang sannan kashe shi, tana mai roƙon jama’a su guji yaɗa labaran da ba su da tushe.
Ta ce ‘yan sanda za su gudanar da cikakken bincike don gano hakikanin abin da ya faru da tsohon shugabannin hukumar shige da ficen.
Hazalika, rundunar ta ce ta fara farautar matar da suka shiga dakin otel din tare da marigayi Parradang, wacce a yanzu ba a san inda take ba, don gano bakin zaren lamarin.
Ta bukaci jama’a su bai wa hukumomi haɗin kai, tana mai tabbatar da cewa za a gudanar da bincike mai zurfi don tabbatar da gaskiya.
'Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban hukumar NIS
Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga suka kashe tsohon shugaban hukumar NIS, David Shikfu Parradang bayan sun bi sahunsa yayin da ya ciro kuɗi daga banki.
Bayan kwace kuɗin, an ce ƴan bindigan da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe shi ba tare da jin tausayinsa ba yayin da jami’an tsaro sun fara bincike kan lamarin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng