Labarin ma'aikacin otel da ya tsinci damin daloli a dakin baƙi kuma ya mayar ya jawo cece kuce

Labarin ma'aikacin otel da ya tsinci damin daloli a dakin baƙi kuma ya mayar ya jawo cece kuce

- Wani ma’aikaci dan Najeriya, Obiefoh Sunday, ya tsinci bandir din daloli da aka bari a lokacin da yake share dakin

- Maimakon ya boye kudin don amfanin kansa, Sunday ya hanzarta kai rahoton lamarin ga shugabannin otal din

- Mutane da yawa sun yi mamakin gaskiyarsa kamar yadda wasu mutane suka ce za su so su saka masa daga aljihunsu

Wani dan Najeriya, Obiefoh Sunday, wanda ke aikin goge-goge a otal din Lagos Continental, ya nuna gaskiya a aikinsa.

Maigidansa, Muhammad Ashraf, a shafinsa na LinkedIn ya rubuta game da yadda saurayin ya samo wasu daloli na Amurka a daya daga cikin dakunan da ya je tsabtacewa bayan bakon da ya sauka a ciki ya tafi.

KU KARANTA KUMA: Daga Abdulsalami zuwa Buhari: Jaddawalin kuɗaɗen da aka ƙwato waɗanda Abacha ya sace daga 1998

Labarin ma'aikacin otel da ya tsinci damin daloli a dakin baƙi kuma ya mayar ya jawo cece kuce
Labarin ma'aikacin otel da ya tsinci damin daloli a dakin baƙi kuma ya mayar ya jawo cece kuce Hoto: LinkedIn/Muhammad Asraf/Lagos Hotel Continental
Asali: UGC

Ba zai wadatar da kansa da rashin gaskiya ba

Yana tsintar kudin, nan take sai mai aikin goge-gogen ya sanar da hukumar otal din halin da ake ciki kuma an hanzarta shigar da kudin cikin asusun kungiyar kudaden da aka rasa masu shi.

Ashraf ya ce yana matukar alfahari da samun mutum kamar Sunday a cikin tawagarsa, yana mai bayyana cewa abin da ya yi ya faranta musu rai duka.

KU KARANTA KUMA: An Kama Hadimin Gwamna Sule Da Wasu Mutum 16 Kan Satar Kayan Gwamnati

Da yawa sun yabe shi

Hoton Sunday da aka wallafa akan dandamalin ya nuno shi dauke da bandir din daloli wanda ke da dala 100 da yawa a ciki.

Kamar yadda yake a lokacin kawo wannan rahoton, rubutun ya tattara ɗaruruwan martani daga mutanen da suka jinjinawa mai aikin goge-goge.

Ga wasu daga cikin martanin a kasa:

Diadem International ya ce:

"Kai, Mai gida ka yi rawar gani sosai ka horar da mutane kuma sun sa ka Alfahari. Obiefor Sunday na gode da gaskiyarka. Muhammad Ashraf mun yi Alkawarin ba shi lada iya karfinmu kafin ranar 5 ga watan Yuni 2021."

Ibine Victor ya ce:

"Na yi farin ciki matuka cewa har yanzu muna da mutanen kirki a cikin masu aikin kula da gida. Allah ya ci gaba da sanya muku albarka."

Gerry Mcblain ya ce:

"Madalla da saurayin, Sunday, amma ka ce an saka kuɗin a cikin asusun kudaden da aka rasa masu shi, shin an tuntuɓi mutumin da ya bar shi a wurin?"

Felix Ulaikere ya ce:

"Sannu da kokari Sunday ... Na san kai mutumin kwarai ne. Dama daga wurin aikinmu na baya ya kasance mai gaskiya a abubuwan da yake yi. Allah ya saka da alheri."

A wani labarin, wani saurayi dan Najeriya mai dauke da shafin Twitter @sarnchos a ranar Talata, 25 ga watan Mayu, ya bayyana yadda wani bahaushe mai kirki ya kasance mai aminci ga danginsa kusan shekaru 30.

A cikin wallafar farko da ya yi a cikin 2019, ya rubutu yadda mutumin da ya haura shekaru 90 a lokacin yake ta kula da dukiyar mahaifinsa tun bayan rasuwar mahaifin nasa a 1992.

@sarnchos ya bayyana cewa tsawon wadannan shekarun, bai taba karbar wani albashi ba amma ya ciyar da kansa daga abubuwan da ya shuka a filin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel