'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Abuja, Sun Hallaka Tsohon Shugaban Hukumar Tsaro

'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Abuja, Sun Hallaka Tsohon Shugaban Hukumar Tsaro

  • Ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun sake yin wata ta'asa a babban birnin tarayya Abuja
  • Miyagun sun hallaka tsohon shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) a safiyar ranar Talata, 4 ga watan Maris 2025
  • David Shikfu Parradang ya rasa ransa ne bayan ƴan bindigan sun bi sahunsa lokacin da ya ciro kuɗi daga banki
  • Bayan karɓe ƴan kuɗin da ke hannunsa, ƴan bindigan sun hallaka shi saboda rashin imanin da suke da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe tsohon shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya (NIS), David Shikfu Parradang.

Ana zargin cewa yan bindigan sun kashe David Shikfu Parradang ne a babban birrnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Ramadan: Ɗan Shugaba Bola Tinubu ya yamutsa siyasar Kano a wurin buɗa bakin azumi

'Yan bindiga sun hallaka Shikfu Parradanga a Abuja
'Yan bindiga sun hallaka tsohon shugaban hukumar NIS Hoto: @Parradang01
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Nakeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kashe Parradang

A cewar wasu majiyoyi, an sace Parradang ne a yankin Area 1 na birnin Abuja da safiyar ranar Talata, 4 ga watan Maris 2025.

Ƴan bindigan sun bi sahun Parradang daga banki inda ya ciro kudi, sannan daga bisani suka karɓe kuɗin daga hannunsa kafin su kashe shi.

Wannan lamarin ya haifar da sabuwar damuwa game da tsaro a babban birnin tarayya Abuja, musamman game da ƙaruwar sace-sacen mutane.

Parradang ya daɗe yana aiki a NIS

Parradang, wanda ya yi aiki a NIS na tsawon shekaru fiye da 30, ya riƙe mukamai daban-daban a faɗin ƙasar nan, ciki har da na shugaban hukumar.

Ya yi aiki a jihojin Kano, Legas, Kwara, Enugu, da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ware sama da Naira biliyan 700 a watan azumi, za a yi muhimman ayyuka

Haka kuma, ya halarci kwasa-kwasai da dama a cikin Najeriya da ma ƙasashen waje.

Domin yabawa aikin da ya yi a hukumar, an ba shi lambar yabo ta ƙasa Officer of the Order of the Federal Republic (OFR).

Me hukumar NIS ta ce kan kisan?

Rahotanni na cewa hukumomin tsaro sun fara bincike kan yanayin da aka sace shi da kashe shi, inda suke ƙoƙarin cafke waɗanda suka aikata laifin.

Hukumar shige da fice ta Najeriya ba ta tabbatar da aukuwar lamarin ba, amma wani jami'i a hedkwatar hukumar da ke a Abuja ya ce gaskiya ne.

“Rahoton gaskiya ne amma dole ne mu jira hukumar shige da fice ta fitar da sanarwa a hukumance."

- Wata majiya

Ƴan bindiga sun hallaka jami'an tsaro a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun hallaka jami'an tsaro na ƴan sa-kai a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, sun kashe babban kwamandan Boko Haram

Ƴan bindigan sun hallaka ƴan sa-kan ne ta hanyar yi musu kwanton ɓauna lokacin da suka bi bayansu bayan sun sace shanu a ƙauyukan Dan Tulu da Rusakde, cikin ƙaramar hukumar Arewa.

Lamarin wanda ya auku a dajin Matankari ya jefa al'ummar yankin cikin jimami sakamakon asarar rayukan jami'an tsaron da aka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng