'Ya Gama Lalata da Buduwa': An Tsinci Gawar Ɗan Sandan Najeriya a Otel ɗin Abuja

'Ya Gama Lalata da Buduwa': An Tsinci Gawar Ɗan Sandan Najeriya a Otel ɗin Abuja

  • Ana fargabar cewa Lawal Ibrahim, wani jami'in dan sanda daga sashen rundunar na Kwali, ya mutu a wani otel da ke Gwagwalada
  • An gano cewa Lawal ya haɗu da Maryam Abba a shafukan sada zumunta watanni uku da suka gabata, inda suka yi sharholiya a otel din
  • Tuni dai aka ce hukuma ta kama Maryam yayin da 'yan sandan suka ki cewa komai game da jami'insu da ya mutu a wannan yanayi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - An samu rahoton rasuwar wani jami'in dan sanda, Lawal Ibrahim, daga sashen rundunar Kwali, a otel ɗin Palasa Guest Inn da ke Gwagwalada.

An ce lamarin ya faru a ranar Alhamis da safe, lokacin da ya kwana a ɗakin otel tare da wata budurwa Maryam Abba.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Rundunar 'yan sanda ta ki cewa komai da aka tsinci gawar jami'inta a dakin otel tare da budurwa
Abuja: Ana fargabar dan sandan Najeriya ya mutu bayan gama lalata da budurwa a dakin otel. Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Abuja: Dan sanda ya gayyaci budurwa otel

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa dan sandan, Lawal da budurwar, Maryam sun haɗu a shafukan sada zumunta watanni uku da suka gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce MAryam Abba, 'yar asalin jihar Jigawa ce, kuma dan sandan ya tura mata kudin mota inda ta same shi a otel din na Abuja.

An ce Lawal da Maryam sun yi lalata da daddare inda ya yi 'zuwa daya', sannan da Asuba budurwar ta tashi dan sandan suka sake komawa 'zagaye na biyu'.

Sai dai lokacin da Maryam ta farka da safe, ta lura cewa Lawal yana numfashi mai sarkewa kuma jikinsa ya daina motsi.

Dan sanda ya mutu bayan 'zagaye na biyu'

An ce Maryam ta yi ƙoƙarin tayar da shi ta hanyar yayyafa ma shi ruwa, amma hakan ya ci tura.

Ganin hakan ya sa aka ce Maryam ta yi ihu ta sanar da manajan otel din, Danlami Palasa, wanda ya kai rahoto ga sashen 'yan sandan Gwagwalada.

Kara karanta wannan

Hamshakin mai kudin duniya, Bill Gates ya fadi babban kuskuren da ya yi a rayuwa

'Yan sanda sun isa otel ɗin kuma sun samu gawar Lawal a ɗakin.

An kai gawarsa Asibitin koyarwa na jami'ar Abuja, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

An gano wasu kayayya a ɗakin, ciki har da abarba, maganin da ake zargin aphrodisiac ne (mai kara karfin maza), cajar waya, da katin shaidar aikin Lawal.

'Yan sanda sun yi gum da mutuwar jami'insu

Tuni dai aka ce 'yan sandan sun kama Maryam kuma ana gudanar da bincike kan lamarin.

Wata majiya daga sashen 'yan sanda na Gwagwalada ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da cewa Maryam tana tsare yayin da ake gudanar da bincike.

Sai dai duk wani yunkuri na samun martani daga kakakin rundunar 'yan sandan FCT, SP Adeh Josephine, ya ci tura yayin da ba ta daukar waya ko mayar da sako.

Matashi ya mutu yana tsaka da lalata da budurwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani matashin ya mutu yayin da yake nuna tsantsar kurewarsa yayin da yake lalata da wata abokiyar sharholiyarsa.

Kara karanta wannan

An rusa gidan da masu garkuwa ke birne mutane, an gano kaburbura 30

Bincike ya nuna cewa matashin ya sha maganin kara karfin maza, wanda aka samu kwalin a cikin dakinsa tare da wasu lemukan kara kuzari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.