Azumi: 'Dan majalisar NNPP Ya Ware Mutane 10,000 Ya Raba Musu Miliyoyin Naira

Azumi: 'Dan majalisar NNPP Ya Ware Mutane 10,000 Ya Raba Musu Miliyoyin Naira

  • 'Dan majalisar wakilai na Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya raba tallafin azumi ga mutum 10,000 domin rage musu radadin rayuwa
  • Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun samu kudi daga ₦10,000 zuwa ₦200,000, yayin da matasa 2,000 a mazabarsa suka samu kayan sana’a
  • Mutane da dama sun jinjinawa Hon. Kofa bisa wannan tallafi da ya saba bai wa al’ummar mazaɓarsa, musamman a lokacin Ramadan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - A wani gagarumin shiri na tallafawa jama’a, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya raba kudi da kayan sana’a ga mutane 10,000 a yankin Kiru da Bebeji na jihar Kano.

Tallafin, d aka shirya domin rage wahalhalun da ake fuskanta a lokacin azumi, ya hada da rabon kudi ga mata da maza, da kuma kayan sana’a ga matasa domin dogaro da kai.

Kara karanta wannan

Bauchi: Miji ya yi wa matarsa dukan tsiya har ta zarce lahira kan abincin Ramadan

Kofa Tallafi
Dan majalisa ya raba tallafi a Kani. Hoto: Hon Abdulmumin Jibrin Kofa PhD
Asali: Facebook

Legit ta tattara bayanai kan yadda aka raba kudi da kayayyakin ne a cikin wani sako da dan majalisar ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban hadimin dan majalisar, Dr. Ahmad Bala Jinjiri ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar 4 ga watan Maris, 2025.

Hon. Kofa ya raba kudi ga mata da maza

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya tallafawa al’ummar mazaɓarsa ta Kiru da Bebeji da kudi domin rage musu radadin azumi.

Mutum 10,000 ne suka ci gajiyar shirin, inda aka raba kudi ₦200,000 ga wasu, ₦100,000 ga wasu, yayin da wasu suka samu ₦50,000, ₦20,000 da kuma ₦10,000.

Shirin tallafin ya kasance wani mataki na rage wahalhalun da ake fuskanta, musamman a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki a kasar nan.

Matasan Kiru/Bebeji sun samu kayan sana’a

Baya ga rabon kudin, Hon. Kofa ya raba kayan sana’a ga matasa 2,000 domin su samu damar dogaro da kansu.

Kara karanta wannan

Ana murnar fara azumi, sanatan Arewa ya shirya gagarumin bikin tallafawa talakawa

Dan majalaisar ya ce wannan na daya daga cikin shirye-shiryen da ya ke aiwatarwa domin habaka tattalin arzikin matasan mazabarsa.

Tallafin ya hada da kayayyakin sana’o’i daban-daban kamar su dinki da sauran sana’o’in da za su taimaka wa matasan wajen inganta rayuwarsu.

Hon. Kofa
Dan majalisa mai wakiltar Kiru da Bebeji. Hoto: Hon Abdulmumin Jibrin Kofa PhD
Asali: Facebook

Jama’a sun yabawa Kofa bisa raba tallafi

Bayan rabon tallafin, jama’a da dama a kafafen sadarwa sun yi yabo ga Hon. Kofa bisa wannan kokari da yake yi don taimakawa al’ummar mazaɓarsa.

Wasu daga cikin jama'ar sun ce Hon. Kofa ya zama abin koyi wajen taimakon jama’a, musamman a irin wannan lokaci da ake bukatar tallafi.

Kungiya ta karrama Kwankwaso a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiyar matasa ta karrama tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a jihar Kano.

Kungiyar ta bayyana cewa Kwankwaso ya kasance shugaba da ya ke karfafa gwiwar matasa a fadin kasar nan, kuma saboda haka ne aka ba shi lambar karramawar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng