Majalisa Ta Damu da Rashin Tsaro a Borno, Ta ba Gwamnatin Tarayya Shawara

Majalisa Ta Damu da Rashin Tsaro a Borno, Ta ba Gwamnatin Tarayya Shawara

  • Majalisar wakilan Najeriya ta nuna damuwa kan halin rashin tsaro da ke addabar wasu yankunan jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas
  • Wani ɗan majalisa daga cikin Borno ya gabatar da ƙuɗiri, ya bayyana halin da mutanen yankunan suke ciki sakamakon hare-haren ƴan ta'adda
  • Majalisar wakilan kasar nan ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta tura ƙarin jami'an tsaro da kayan agaji domin tallafawa mutanen yankunan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya kan matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a wasu yankunan jihar Borno.

Majalisar wakilan ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta aika sojoji zuwa wasu yankunan jihar Borno da suke fama da matsalar rashin tsaro.

Majalisar wakilai ta koka kan rashin tsaro Borno
Majalisar wakilai ta bukaci a tura karin jami'an tsaro a Borno Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta rahoto cewa majalisar wakilan ta yi wannan kiran ne yayin zamanta na ranar Talata.

Kara karanta wannan

Zance ya kare, kotun ƙoli ta yanke hukunci kan bukatar tsige 'yan Majalisa 27

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gabatar da ƙudiri kan rashin tsaro a Borno

Majalisar ta cimma wannan matsayar ne biyo bayan amincewa da ƙudirin gaggawa da ɗan majalisa mai wakiltar Askira-Uba/Hawul daga jihar Borno, Midala Balami, ya gabatar.

Da yake bayani kan kudirin, Midala Balami, na jam’iyyar PDP, ya bayyana yadda ƴan ta'addan Boko Haram suka kai hari kan ƙauyukan Jibwuwhi da Yarkawa a ƙaramar hukumar Hawul ta jihar Borno.

Wannan harin ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da lalata dukiyoyi, tare da tilasta wa mazauna waɗannan yankunan yin hijira daga gidajensu.

"Hare-haren ƴan ta'adda na ci gaba da faruwa duk da irin ƙoƙarin da hukumomin tsaro ke yi."
"Wannan lamarin yana sanya mutane cikin fargaba, rasa hanyoyin samun abinci da kuma jefa rayuwar jama'a cikin hatsari."

- Midala Balami

Wace shawara majalisa ta ba da?

Bayan amincewa da ƙudirin, majalisar wakilai ta buƙaci rundunar sojojin Najeriya, ƴan Sandan Najeriya, da sauran hukumomin tsaro da su tura jami’an tsaro zuwa yankunan nan take.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi wa 'yan binɗiga kofar rago, sun hallaka miyagu

Ta buƙaci a tura jami'an ne domin ƙarfafa tsaro a Jibwuwhi da Yarkawa, da sauran yankunan da ke cikin barazana a ƙaramar hukumar Hawul, domin hana sake kai hare-hare.

Haka kuma, majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya, ta hannun Ma’aikatar harkokin jin ƙai da rage talauci, tare da hukumar NEMA da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Borno, da su gaggauta samar da kayan agaji ga mutanen yankunan.

Majalisar ta buƙaci a tura kayan agaji a yankunan da suka haɗa da abinci, magunguna domin tallafawa mutane, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Bugu da ƙari, majalisar ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta ƙarfafa shirin yaƙi da ta’addanci a Borno, tare da inganta samun bayanan sirri da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da ƙungiyoyin sa-kai, domin hana sake kai hare-hare a mazaɓar Askira-Uba/Hawul.

Majalisa ta amince da buƙatar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilan Najeriya ta amince da buƙatar da shugaban ƙasa ya gabatar mata na ƙara kasafin kuɗin shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi taron dangi kan 'yan ta'adda, sun hallaka miyagu masu yawa

Majalisar ta amince shugaba Bola Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin shekarar 2025 daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2. sakamakon karin kuɗin shiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng