Zance Ya Ƙare, Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukunci kan Bukatar Tsige Ƴan Majalisa 27
- Bayan shafe tsawon lokaci ana shari'a a kotuna, kotun kolin Najeriya ta warware rikicin Majalisar dokokin jihar Ribas
- Kotun mafi daraja ta sallami ƙarar da Gwamna Simi Fubara ya shigar yana rokon ta tsige ƴan Majalisa 27 da suka sauya sheƙa zuwa APC
- A zaman ranar Litinin, 10 ga watan Fabrairu, kotun ta kuma ci tarar mai girma gwamna Naira miliyan biyu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kotun Koli ta yi watsi da karar da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya shigar yana neman a tsige ‘yan majalisar dokoki guda 27 saboda zargin sun sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
Gwamna Fubara ya ɗaukaka ƙara har zuwa kotun ƙoli domin a tsige ƴan Majalisa 27 masu goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike kan sauya shekar da suka yi.

Kara karanta wannan
Ba a gama da ƙudirin haraji ba, Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon ƙarin harajin NPA

Asali: UGC
Gwamna Fubara ya janye ƙarar da ya shigar
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta yi fatali da ƙarar ne bayan gwamnan ya sanar da janyewa a zaman yau Litinin, 10 ga watan Fabrairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Siminalayi Fubara ya shaidawa kotun ƙoli cewa ya janye ƙarar ne saboda abubuwan da suka sa ya kawo ƙarar sun riga da sun wuce.
Ƴan Majalisar Ribas 27 sun yi nasara a kotu
Kwamitin alkalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a Uwani Abba-Aji ta yanke hukuncin cewa kotu ta ci tarar gwamnan Naira miliyan biyu (N2m).
Lauyan gwamnan, Yusuf Ali (SAN), ya nemi janye karar tun da farko, yana mai cewa batun ya riga ya zama tarihi.
Sai dai lauyoyin bangaren ‘yan majalisar da ke karkashin jagorancin Martin Amaewhule, Wole Olanipekun (SAN) da Joseph Daudu (SAN), ba su yi jayayya da janye karar ba.
Amma sun bukaci kotu da ta kori karar gaba daya, ba wai kawai a janye ta ba, sannan kuma suka buƙaci a ci tarar gwamnan N2m inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan
"Najeriya ta yi Rashi," Tinubu ya kaɗu da Allah ya yi wa fitaccen malamin Musulunci rasuwa
Yadda kotun baya suka yanke hukunci
A ranar 10 ga Oktoba, 2024, ƙotun ɗukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da Gwamna Fubara ya shigar kan ‘yan majalisar 27, tana mai cewa gwamnan ba shi da wata hujja.
A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Joseph Oyewole ya bayyana cewa tun da gwamnan ya janye kansa daga karar da kansa, yana nufin ya aminta da hukuncin babbar kotun tarayya.
A sakamakon haka, kotun ɗaukaka ƙara ta hana Fubara yin katsalandan a harkokin Majalisar dokokin jihar Ribas.
Haka kuma, kotun ta hana shi dakatar da kudaden majalisar, ta kuma haramta masa tsige cire magatakarda da mataimakinnsa.
An umarci Fubara ya sake gabatar da kasafi
Kotun ta umarce shi da ya sake gabatar da kasafin kudin jihar ga majalisar karkashin Amaewhule, kamar yadda hukuncin Mai Shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya ya yi hukunci.
Bayan haka kuma Gwamna Fubara ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli da a yau Litinin ta kori ƙarar bayan ya janye kansa daga cikin shari'ar.
Rikici ya ɓarke a sakatariyar PDP a Ribas
A wani labarin da ya shafi Ribas, kun ji cewa rigima ta kaure a babbar sakatariyar PDP da ke birnin Fatakwal har da harbe-harben bindiga.
Rahotanni sun nuna cewa an gwabza faɗa ne tsakanin magoya bayan Gwamna Siminalayi Fubara da ministan Abuja, Nyesom Wike.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng