Dakarun Sojoji Sun Yi Wa 'Yan Bindiga Kofar Rago, Sun Hallaka Miyagu

Dakarun Sojoji Sun Yi Wa 'Yan Bindiga Kofar Rago, Sun Hallaka Miyagu

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara a yaƙin da suke yi da ƴan bindiga a jihar Zamfara da ke fama da matsaloli
  • Sojojin sun kai wani samame kan ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Anka, inda suka hallaka tsageru guda huɗu
  • Jami'an tsaron bayan sun fatattaki ƴan bindigan, sun kuma samu nasarar cafke wani guda ɗaya daga cikimsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasarar kashe ƴan bindiga huɗu a jihar Zamfara.

Dakarun sojojin sun kuma cafke wani ɗan bindiga guda ɗaya a yayin wani samame da suka kai da daddare a garin Nasarawa, cikin ƙaramar hukumar Anka ta jihar Zamfara.

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Zamfara
Dakarun sojoji sun hallaka 'yan bindiga hudu a Zamfara Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi taron dangi kan 'yan ta'adda, sun hallaka miyagu masu yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka kai samamen

Majiyoyin sirri sun bayyana cewa an kai samamen ne a daren ranar Lahadi, 9 ga watan Fabrairun 2025.

Farmakin wanda ya ci gaba da gudana har zuwa wayewar gari, an kai shi ne da nufin fattakar ƴan bindigan da suka addabi yankin.

Dakarun sojojin sun ƙaddamar da farmakin ne bayan samun bayanan cewa ƴan ta'adda na ɓuya a yankin.

Sojojin sun mamaye sansanin ƴan bindigan inda suka yi musayar wuta mai tsanani.

Daga ƙarshe, sojoji sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga mutum huɗu, yayin da suka cafke guda ɗaya da ransa.

Sojoji sun kashe ƴan bindiga

Daga cikin waɗanda aka kashe, akwai wani mutum da aka daɗe ana zargi da hannu a ayyukan ta’addanci a garin Nasarawa.

A halin yanzu, ɗan bindigan da aka kama yana hannun hukumomi, kuma ana ci gaba da bincike a kansa don samun ƙarin bayani kan ayyukan ta’addancin da suke gudanarwa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya fadi nasarorin da aka samu kan 'yan bindiga a jihar

Wannan nasara na daga cikin ƙoƙarin da sojojin Najeriya ke yi domin kawo ƙarshen ƴan bindiga a yankin, tare da dawo da zaman lafiya.

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan ƴan ta'addan da ke tayar da zaune tsaye a jihar Zamfara.

Sojojin sun kashe ƴan ta'adda 44 tare da raunata da dama daga cikinsu a wani farnaki da suka kai musu a maɓoyarsu.

Dakarun sojojin sun nuna ƙwarewa da bajinta a musayar wutar da suka yi da ƴan ta'addan waɗanda ke addabar mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng