Shirin Karin Kuɗin Kira da Sayen Data a Najeriya Ya Gamu da Cikas, Majalisa Ta Tsoma Baki

Shirin Karin Kuɗin Kira da Sayen Data a Najeriya Ya Gamu da Cikas, Majalisa Ta Tsoma Baki

  • Majalisar Wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da shirinta na ƙarin kudin kira da sayen data a Najeriya
  • Ta ɗauki wannan matakin ne a zaman Majalisar na yau Talata, 11 ga watan Fabrairu, 2025 bayan amincewa da kudirin da Obuku Offorji ya gabatar
  • Tun farko hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta amince kamfanonin sadarwa kamar MTN da Airtel su ƙara kuɗin kira da kaso 50%

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Majalisar Wakilai ta tsoma baki kan yunƙurin gwamnatin tarayya da kamfanonin sadarwa na ƙarin kudin kira da sayen data a Najeriya

Majalisar ta bukaci Ministan sadarwa, Bosun Tijani, da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), su dakatar da shirin karin kudin sadarwa har sai an inganta sabis.

Majalisar Wakilai.
Majalisa ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin karin kudin kira Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa matakin ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa da dan majalisa, Hon. Obuku Offorji ya gabatar a zaman yau Talata.

Kara karanta wannan

Ba a gama da ƙudirin haraji ba, Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon ƙarin harajin NPA

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanoni na shirin kara kuɗin kira

Da yake gabatar da kudirin, Offorji ya tunatar da cewa a taron masu ruwa da tsaki a ranar 8 ga Janairu, ministan ya ce kamfanonin sadarwa na shirin kara kuɗin kira.

Ministan ya ce ana ci gaba da tattaunawa saboda wasu daga cikin kamfanonin suna kokarin kara kudin da kashi 100.

Sai dai ya ce karin ba zai kai haka ba, yana mai cewa hukumar NCC za ta yi nazari kan ƙarin da ya dace a yi duba da matsin da al'umma ke ciki.

Amma dan majalisar ya kalubalanci dalilan karin da kamfanonin sadarwa suka bayar, wanda suka hada da tsadar kayan aiki, inganta hanyoyin sadarwa, da sauran su.

Kamfanonin sun jima suna neman dama

Hon. Offorji ya ce tun sama da shekaru 11, kungiyoyin kamfanonin sadarwa watau ALTON da ATCON suka matsa lamba domin ganin an kara kudin sadarwa.

A cewarsu, suna bukatar hakan ne saboda hauhawar farashin kayayyaki da kuma asarar da suke fuskanta sakamakon karyewar darajar Naira a kasuwar musaya.

Kara karanta wannan

"Jihohi za su fara gasa," Gwamnati ta ce kudirin haraji zai farfado da tattalin arziki

Kungiyar kare hakkin masu amfani da sadarwa ta Najeriya ta soki shirin karin kudin, tana mai bayyana shi a matsayin rashin tausayi da kuma karin nauyi ga al’umma.

Majalisa ta tattauna kan ƙarin kudin

Da yake jawabi a zauren Majalisar Wakilai, Hon. Offirji ya ce:

"Dole ne kamfanonin sadarwa su inganta ayyukansu, wanda ‘yan Najeriya ke bukata, kafin su dauki matakin kara farashinsu.
"Karin kudin zai kara dagula halin da talakawa ke ciki, ya haifar da karin talauci, ya hana mutane samun damar yin amfani da fasaha don ci gaban tattalin arziki, kuma zai fi shafar masu karamin karfi."

Majalisa ta buƙaci a dakatar da shirin ƙarin

Ya kara da cewa samun sadarwa mai araha na da matukar muhimmanci ga cigaban bangarori masu tafiya da zamani kamar banki, ilimi, kiwon lafiya, noma da shugabanci.

Haka kuma, karin kudin na iya hana ‘yan kasuwa da ke dogaro da data mai rahusa damar yin sana’o’in su ta yanar gizo, kamar yadda The Nation ta kawo.

Kara karanta wannan

'Gwamnati ta kawo sabon haraji da zai jawo tashin farashi,' Saraki ya tono magana

Bayan muhawara kan kudirin, Majalisa ta umarci ministan sadarwa da NCC s] dakatar da shirin ƙarin kuɗin kira har sai kamfanoni sun inganta sabis di sadarwa.

Majalisa ta buƙaci a ƙara turawa Borno sojoji

Kun ji cewa Majalisar Wakilai ta nuna damuwa kan halin tashin tsaro da ake fama da shi a wasu sassan jihar Borno.

Majalisar wakilan ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta aika sojoji zuwa wasu yankunan jihar Borno domin tsare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262