Ba a Gama da Kudirin Haraji ba, Gwamnatin Tinubu Ta Ɓullo da Sabon Ƙarin Harajin NPA

Ba a Gama da Kudirin Haraji ba, Gwamnatin Tinubu Ta Ɓullo da Sabon Ƙarin Harajin NPA

  • Kungiyar masana'antu ta kasa watau MAN ta caccaki shirin ƙarin harajin shigo da kaya ta tashohin ruwa da kaso 15%
  • Shugaban MAN na kasa, Segun Ajayi Kadir ya bayyana cewa yunkurin NPA na ƙarin harajin bai zo a lokacin da ya kamata ba
  • Ya ce idan aka yi ƙarin zai jawo ƙarin matsaloli ga masana'antu kamar rage yawan kayan da suke kerawa, rage ma'aikata da ƙara farashin kayansu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ƙungiyar Masana’antu ta Najeriya (MAN) ta soki karin kashi 15 cikin 100 na kudin haraji da hukumar tashoshin jiragen ruwa (NPA) ke shirin ƙaƙaba masu.

A ranar 6 ga Fabrairu, NPA ta bayyana cewa an amince mata ta kara harajin da kashi 15% domin bunkasa ababen more rayuwa da kuma sabunta kayan aiki.

Tashohin ruwa.
"Ku canza tunani," Kungiyar MAN ta nuna damuwa da karin harajin da NPA ke shirin yi Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Wannan shi ne karo na farko da aka sake duba wannan haraji tun shekarar 1993, kamar yadda jaridar The Cable ta tattaro.

Kara karanta wannan

'Gwamnati ta kawo sabon haraji da zai jawo tashin farashi,' Saraki ya tono magana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

MAN ta soki shirin ƙara kuɗin harajin NPA

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Darakta-Janar na MAN, Segun Ajayi-Kadir, ya ce masana’antu a Najeriya sun jima suna fuskantar matsaloli da dama.

Ya bayyana cewa wannan karin ya zo a lokacin da bai dace ba, domin ƴan kasuwa na fama da hauhawar farashin kayan aiki, tsadar canjin kudade waje, da rashin tabbas a tattalin arziki.

Ajayi-Kadir ya nuna damuwa kan yanayin tattalin arziki, wanda ke fama da hauhawar farashin kayayyaki, matsalar canjin kudade, da kuma raguwar yawan sarrafa kayayyaki a masana’antu.

Ya ce tashoshin jiragen ruwa suna da matukar muhimmanci ga harkokin kasuwanci na kasa da kasa, kuma su ne ke da tasiri wajen rage ko kara tsadar kasuwanci.

Ƙarin haraji: Kayayyaki za su kara tsada

"A cewar Hukumar Kula da Cinikayya ta Majalisar Dinkin Duniya (UNCTAD), kashi 80% na kayayyakin da ake amfani da su a Najeriya ana safararsu ta teku.

Kara karanta wannan

"Muna da hujjoji," Jigon APC ya cire kunya, ya ƙaryata tsohon shugaba Muhammadu Buhari

"Sannan kuma kashi 70% na jimillar kayayyakin da ake shigowa da fita da su a Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya duk na Najeriya ne. Hakan na nuna muhimmancin tashoshin ruwa wajen saukaka harkokin kasuwanci.
"Kudaden da ake biya a tashoshin ruwa suna shafar kasuwanci kai tsaye, domin mafi yawan kayan aiki da injinan masana’antu ana shigo da su ne ta wadannan tashoshi.
"Don haka karin haraji zai haifar da tashin farashin sarrafa kayayyaki, karin hauhawar farashi a kasa da kuma rage karfin kayayyakin da ake kerawa a cikin gida."

- Segun Ajayi-Kadir.

MAN ta bukaci gwamnatin Tinubu ta dakata

Ajayi-Kadir ya ce wannan karin zai kara jefa masana’antu cikin matsi, wanda zai iya haddasa rage yawan kayan da ake sarrafawa, har ma da rasa ayyukan yi.

Darakta-Janar na MAN ya bukaci gwamnati ta hannun NPA da ta dakatar da shirin kara harajin, ta hada kai da masu ruwa da tsaki domin nemo hanyoyin samar da kudaden shiga.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gari gari, sun kashe bayin Allah tare da sace mutane sama da 100

Gwamnati ba za ta ƙayyade farashi ba

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa ba ta da hurumin kayyade farashin kayayyaki.

Shugaban hukumar kare hakkin masu sayen kaya watau FCCPC ne ya bayyana hakan, ya buƙaci duk wanda aka tauye hakkinsa ya shigar da ƙorafi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262