'Gwamnati Ta Kawo Sabon Haraji da zai Jawo Tashin Farashi,' Saraki Ya Tono Magana

'Gwamnati Ta Kawo Sabon Haraji da zai Jawo Tashin Farashi,' Saraki Ya Tono Magana

  • Kungiyar NECA da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, sun soki sabon harajin kashi 4% da Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ƙara
  • NECA ta bayyana cewa sabon harajin zai ƙara dagula tattalin arzikin ƙasa, wanda ya riga ya kasance cikin matsala a halin yanzu
  • Saraki ya bukaci gwamnati ta sake duba lamarin, yana mai cewa harajin zai haifar da tashin farashin kaya da kuma matsin lamba ga 'yan kasuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ƙaddamar da sabon harajin kashi 4% a harkar kayayyaki bisa dokar da aka amince da ita a shekarar 2023.

Kungiyar NECA da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, sun nuna rashin amincewarsu da sabon haraji, suna cewa hakan zai ƙara wahalar da ‘yan kasuwa da 'yan kasa.

Kara karanta wannan

"Jihohi za su fara gasa," Gwamnati ta ce kudirin haraji zai farfado da tattalin arziki

Saraki
Saraki ya bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da sabon harajin kwastam. Hoto: Bayo Onanuga|Abubakar Bukola Saraki
Asali: Facebook

Sanata Abubakar Bukola Saraki ya bukaci gwamnatin tarayya ta janye harajin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NECA: Sabon haraji zai dagula tattali

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kungiyar NECA ta ce matakin bai dace da halin da ake ciki ba kuma zai durkusa harkokin kasuwanci da tattalin arzikin ƙasa.

Shugaban kungiyar NECA, Adewale-Smatt Oyerinde, ya bayyana cewa sabuwar dokar kwastam ta 2023 wacce ta ƙunshi karin harajin kashi 4% ba ta dace ba a wannan lokacin ba.

Adewale-Smatt Oyerinde ya ce:

"Tattalin arzikin Najeriya na fuskantar ƙalubale da yawa, ciki har da karin haraji, manufofin gwamnati marasa tabbas da matsalolin kasuwanci.
"Wannan sabon haraji zai ƙara tsadar kayayyaki da rage ayyukan yi."

A cewarsa, ƙara harajin zai haifar da hauhawar farashi, rage yawan kayayyakin da ake saye, da ƙara rikita kasuwanci.

"Ma’aikata da ‘yan kasuwa za su fuskanci kalubale, sannan farashin kayayyaki zai tashi, wanda zai shafi al’ummar ƙasa gaba ɗaya,"

Kara karanta wannan

"Muna da hujjoji," Jigon APC ya cire kunya, ya ƙaryata tsohon shugaba Muhammadu Buhari

- Adewale-Smatt Oyerinde

Saraki ya bukaci a janye harajin kwastam

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana rashin amincewarsa da karin harajin da Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ƙara.

A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa, Saraki ya ce:

"Sabon harajin zai zama ƙarin nauyi a kan ‘yan kasuwa da masu sayayya."

Ya ci gaba da cewa:

"Najeriya na shigo da kayayyaki da darajarsu ta kai Naira tiriliyan 71 a kowace shekara. Idan aka ƙara kashi 4% na FOB, hakan na nufin an ƙara harajin Naira tiriliyan 2.84.
"Shin Kwastam na buƙatar wannan adadi domin gudanar da aikinta?"

Bukola Saraki ya bukaci gwamnatin tarayya ta janye harajin nan take domin a cewarsa, lamarin bai dace da kudirin Tinubu na saukaka tsadar rayuwa ba.

A yanzu haka dai kallo ya koma kan gwamnatin tarayya domin ganin ko za ta saurari koken dakatar da karin harajin.

Kara karanta wannan

'Ka taka masa birki': An kai karar El Rufai gaban Nuhu Ribadu, an hango hatsarin kalamansa

Gwamnati za ta tallafawa mata a jihohi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fitar da wani shiri na musamman domin tallafawa mata a Najeriya.

Ministar harkokin mata ta tarayya ta bayyana cewa mata kusan miliyan biyar za su ci gajiyar shirin a dukkan jihohin Najeriya 36 domin bunkasa tattalin su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng