"Jihohi za Su Fara Gasa," Gwamnati Ta ce Kudirin Haraji zai Farfado da Tattalin Arziki
- Gwamnatin tarayya ta kara kwantar da hankulan 'yan Najeriya a kan kudirin harajin da shugaban kasa, Bola Tinubu ya mika wa majalisa
- Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ya tabbatar da cewa jihohi za su amfana da sababbin kudirorin wajen bunkasa arziki
- Gwamnatin ta kuma musanta zargin cewa an bijiro da kudirin ne domin muzgunawa wata shiyya, tare da kokarin fifita wata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kudirin harajin shugaba Bola Ahmed Tinubu zai haifar da gasa mai kyau a tattalin arziki tsakanin jihohi.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a jiya, yayin da ake ci gaba da dambarwa a kan batun.

Kara karanta wannan
'Gwamnati ta kawo sabon haraji da zai jawo tashin farashi,' Saraki ya tono magana

Asali: Facebook
Ya shaidawa jaridar The Nation cewa kudirin dokokin garambawul na haraji da aka gabatar an tsara su ne domin sake daidaita kasar bisa tafarkin dorewar ci gaba a tattalin arziki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta musanta zargin cutar da Arewa
Mohammed Idris ya musanta fargabar da wasu ke nuna wa cewa sabon tsarin haraji zai fi cutar da wasu yankuna, musamman Arewacin Najeriya.
Ministan ya ce:
“Akasin abin da wasu ke tunani, sabon tsarin haraji an tsara shi ne domin mayar da Najeriya kan tafarkin dorewar ci gaba, kawar da cin hanci, kawo karshen haraji mai yawan yawa, da kuma inganta gudanar da haraji. Ba a tsara shi don cutar da wata kabila ko yanki ba.”
Kusoshin gwamnatin Tinubu sun kare kudirin haraji
Shi ma shugaban kwamitin shugaban kasa kan manufofin kudi da garambawul na haraji, Taiwo Oyedele, ya kare kudirin, ya na mai cewa shirin zai kara habaka kudaden shiga na gwamnati a dukkan matakai.
Sabon tsarin karbar harajin VAT da aka gabatar zai canza yadda ake rarraba kudaden shiga domin ya bayyana ainihin harkokin tattalin arziki na kowace jiha.
Yadda gwamnati ke son raba haraji
A cewar Oyedele, a karkashin sabon tsarin, kudaden VAT za a rarraba su ne bisa la’akari da inda ake cinye kayayyaki da aiyuka, maimakon inda ake kera su.
Oyedele ya ce:
“Maimaikon cewa saboda kamfanin da ke kera kayan sha yana da hedkwata a Legas, to a nan ne duk kudaden VAT za su taru, za mu duba inda aka aika da kayayyakin.”
Gwamna ya koma goyon kudirin haraji
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa ya gano muhimmancin amfanin kudirin haraji da gwamnatin Shugaban kasa, Bola Tinubu ta bijiro da su.
Ya kara da cewa tattaunawar da aka yi da jami'an gwamnati ya kara haske a kan tsarin tattalin azikin kasa, inda ya bayyana cewa ya kamata gwamnonin Arewa su rungumi sabuwar manufar gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng