MRS: An Sauke Farashin Man Fetur a Jihohin Najeriya

MRS: An Sauke Farashin Man Fetur a Jihohin Najeriya

  • Rahotanni sun nuna cewa kamfanin man fetur na MRS ya rage farashin litar mai a dukkanin gidajen man sa a fadin Najeriya
  • Kamfanin ya bayyana sabon farashin saida litar fetur a yankunan Kudu maso Yamma, Arewa maso Yamma da sauran sassan kasar nan
  • Rage farashin man ya biyo bayan sauke farashin da matatar Dangote da ke Legas ta yi daga N950 zuwa N890 a ranar 1 ga watan Fabrairu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Kamfanin mai na MRS ya rage farashin man fetur a gidajen man sa, inda ya bayyana sabon farashi a Legas da sauran jihohi.

Rage farashin ya biyo bayan saukar kudin litar mai a matatar Dangote ya yi a kwanakin baya yayin ya yi haɗin gwiwa da MRS.

Kara karanta wannan

Ana zargin akwai lauje cikin naɗi da aka kama jami'in NIS ɗauke da manyan makamai

MRS ya rage farashin man fetur
MRS ya rage farashin man fetur Hoto: @MRSOilNigeria
Asali: Twitter

Kamfanin ya bayyana hakan ne a shafinsa na X a ranar Litinin, yana mai cewa yana sayar da fetur mai inganci a duk yankunan ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon farashin man MRS a Najeriya

MRS ya sanar da rage farashin litar man fetur da N10 a fadin Najeriya, ma'ana zai rika sayar da litar fetur a kan N925 a jihar Legas.

Business Day ta wallafa cewa kamfanin MRS ya bayyana sabon tsarin farashin man fetur, inda ya tabbatar da cewa zai rika sayar da mai kamar haka:

  • Kudu maso Yamma: N935
  • Jihohin Arewa: N945
  • Kudu maso Gabas: N955
  • Legas: N925

A cewar kamfanin:

“Farashin na iya bambanta a yankuna, amma inganci ba zai bambanta ba —muna samar da fetur mai inganci wanda ke kara lafiyar injin abin hawa.”

Kamfanin ya kuma buƙaci abokan hulda da su kai ƙorafi idan sun samu wani daga cikin gidajen man sa na sayar da fetur sama da farashin da aka ayyana.

Kara karanta wannan

Ba a gama da ƙudirin haraji ba, Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon ƙarin harajin NPA

Tasirin matatar Dangote kan saukar farashi

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur daga N950 zuwa N890 a ranar 1 ga watan Fabrairu, 2025.

Dangote ya ce matakin ya biyo bayan raguwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya da kuma sauyin yanayin kasuwancin makamashi na duniya.

A cewar jami’in hulɗa da jama’a na matatar Dangote, Anthony Chiejina rage farashin na daga cikin matakan da kamfanin ke ɗauka don saukaka wa ‘yan Najeriya.

Masana na ganin matakin da matatar Dangote ta dauka ya yi tasiri wajen sanya kamfanin MRS sauke farashin.

Tasirin rage farashi ga 'yan kasa

Rage farashin man fetur da Dangote da MRS suka yi zai taimaka wajen rage tsadar rayuwa da inganta tattalin arziki a Najeriya.

Masana tattalin arziki sun ce matakin zai rage farashin sufuri da haɓaka harkokin kasuwanci, musamman ga ‘yan kasuwa da ke dogara da man fetur wajen gudanar da ayyukansu.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga sama da 100 suka taru wajen sace Janar Tsiga a Katsina

Dangote ya ce kamfanin zai ci gaba da bibiyar yanayin kasuwancin makamashi don tabbatar da cewa farashin man fetur yana sauka yadda ya kamata don amfanin ‘yan ƙasa.

Tinubu zai raba tallafi ga mata

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta raba tallafi ga mata kusan miliyan biyar a fadin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa an samar da tallafin ne domin rage radadin rayuwa ga 'yan Najeriya da suke fama da matsalolin tattali bayan cire tallafin mai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng