Ana Zargin Akwai Lauje cikin Naɗi da Aka Kama Jami'in NIS Ɗauke da Manyan Makamai
- Dakarun ƴan sanda sun kama wani jami'in hukumar shige da fice watau NIS ɗauke da bindigogi da alburusai a birnin Abuja
- An kama wanda ake zargin a yankin Zuma yau Litinin da tsakar rana bayan ya kasa bayar da cikakken bayani kan makaman da ke tare da shi
- Kwamishinan ƴan sandan Abuja, CP Olatunji Disu ya tabbatar da cafke jami'in na NIS, kuma ya ce ana kan bincike kan lamarin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Jami’an rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja sun kama wani ma’aikacin Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) dauke da makamai da alburusai iri-iri.
An cafke wanda ake zargin, wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba, a yankin Zuma da ke cikin Abuja da tsakar rana a ranar Litinin.

Asali: Twitter
Rahotan jaridar The Nation ya nuna cewa jami’in ya gaza bayar da gamsasshen bayani kan yadda ya samu wadannan makamai da kuma inda yake kokarin kai su.

Kara karanta wannan
Yan ta'adda sun firgita, an fara neman gwamnati ta karbi tuban jigo a sansanin Turji
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin jami'in NIS da safarar makamai
Wannan ya sa aka fara zarginsa da safarar makamai ga ‘yan ta’adda kuma dakarun ƴan sanda suka yi ram da shi, a rahoton Punch.
Majiyoyi sun bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri daga wasu masu bayar da rahoto dangane da wani mutum da ya bace.
An tattaro cewa makaman da aka kwato daga hannunsa sun hada da bindigogi da wasu makamai masu haɗari.
Yan sanda sun kwace manyan makamai
Wata majiya ta ce:
"Makaman da aka kwace a hannunsa sun haɗa da bindigun AK-47 guda hudu, CZ Scorpion magazine guda hudu, bindigogi guda biyu na CZ Scorpion, harsasai nau’in 139mm, da bindigogin hannu biyu na Diakon da CZ."
Kwamishinan Abuja, CP Olatunji Disu, ya tabbatar da kama jami'in hukumar NIS ɗauke da makamai.
Ya bayyana cewa yanzu haka ana masa tambayoyi kan makaman da aka gani a tattare da shi kuma rundunar ƴan sanda za ta fitar da sanarwa a hukumance nan gaba.
"Yanzu haka an kawo wanda ake zargi gabana kuma ana yi masa tambayoyi. Abin da zan uya tabbatar maku da shi kenan a yanzu," in ji Disu.
Yan sanda sun murkushe yan bindiga
A wani labarin, kun ji cewa dakarun ƴan sanda a jihar Katsina sun samu nasarar ragargaza ƴan bindiga tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa dakaru sun kashe ƴan bindiga 11 tare da ceto mutane 85 da aka yi garkuwa da su a Janairun 2025.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng