Gwamnatin Tinubu za Ta Raba Tallafi ga 'Yan Najeriya Kusan Miliyan 5
- Gwamnatin tarayya na shirin tallafa wa mata miliyan 4.5 a fadin kasar nan a karkashin wani shiri da za a yi hadaka da bankin duniya
- Ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bukaci daukar mataki cikin gaggawa don aiwatar da shirin ba tare da bata lokaci ba
- Rahotanni sun nuna cewa bankin Duniya ya amince da bayar da tallafin Dala miliyan 500 domin aiwatar da shirin a fadin Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya, ta hannun ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma, ta bayyana shirin tallafa wa mata miliyan 4.5 a fadin Najeriya.
Tallafin wanda ke karkashin shirin tallafawa mata na NFWP-SU zai bai wa mata damar samun ci gaba ta fuskar kasuwanci, ilimi da sauransu.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa an amince da shirin tun a watan Yuni 2023, amma an samu jinkirin aiwatarwa na watanni 18, wanda hakan ya sa minista ta bukaci a gaggauta fara aikin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shirin zai tallafa wa mata a fannonin rayuwa
Ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana cewa shirin zai taimaka wa miliyoyin mata su samu ci gaba a fannoni daban-daban na rayuwa.
Ta kara da cewa gwamnatin tarayya na daukar matakai domin tabbatar da cewa kowace mace da aka tsara za ta ci moriyar shirin ba za a bar ta a baya ba.
Hakazalika, babban sakatariyar ma’aikatar, Dr. Maryam Keshinro, ta ce hada kai tsakanin gwamnati da sauran bangarori ne zai taimaka wajen samun nasarar shirin.
Ta ce mata su ne ginshikin al’umma, kuma idan aka basu dama za su taka rawar gani wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.
Gwamnati za ta yi aiki tare da jihohi
Ministar ta bukaci kwamishinonin harkokin mata na jihohi su hanzarta daukar kwararrun ma’aikata da za su jagoranci aiwatar da shirin a matakin jiha.
Ta ce dole ne kowace jiha ta fitar da tsari da jadawalin yadda za ta aiwatar da shirin domin cimma manufa cikin lokaci.
Sannan ta ce gwamnati ta dauki nauyin tabbatar da shirin ya yi nasara domin amfanin mata da tattalin arzikin kasa.
Alakar shirin da gwamnatin Tinubu
An tabbatar da cewa shirin NFWP-SU wani bangare ne na shirin gwamnatin shugaba Bola Tinubu wanda ke da nufin tallafa wa mata miliyan 10 a Najeriya.
Wannan ne karo na biyu da Bankin Duniya ke amincewa da irin wannan lamuni a karkashin gwamnatin Tinubu, wanda hakan ke nuna goyon bayansa ga ci gaban mata.
A karshe, ministar ta ce nasarar mata miliyan 4.5 da za su amfana da shirin, ba wai nasara ce gare su kadai ba, har da nasarar Najeriya gaba daya.
Ta bukaci duk masu ruwa da tsaki su hada kai don tabbatar da cewa shirin ya cimma burinsa tare da kawo sauyi ga rayuwar miliyoyin mata a kasar nan.
An tallafawa matasa a jihar Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta fitar da makudan kudi har Naira miliyan 400 domin tallafawa matasa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce kowane matashi da ya samu shiga shirin zai samu tallafin Naira miliyan daya domin fara sana'ar noma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng