Yadda 'Yan Bindiga Sama da 100 Suka Taru wajen Sace Janar Tsiga a Katsina
- Ana cigaba da samun bayanai kan sace tsohon daraktan hukumar NYSC, Manjo Janar Ibrahim Tsiga (mai ritaya) a gidansa
- Wasu rahotanni sun nuna cewa mazauna yankin sun ce sun yi kira ga hukumomi kafin harin amma ba a dauki mataki ba
- Yayin da ake cigaba da jiran matarnin jami'an tsaron Najeriya, har yanzu rundunar ‘yan sanda ba ta fitar da sanarwa kan lamarin ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Matsalar garkuwa da mutane a Najeriya na ƙara ƙamari, yayin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka sace tsohon daraktan hukumar NYSC.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an sace Manjo Janar Ibrahim Maharazu Tsiga (Mai ritaya) a daren Laraba a gidansa da ke ƙaramar hukumar Bakori, Jihar Katsina.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi tsaurin ido, sun yi garkuwa da Birgediya Janar Maharazu Tsiga

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa mazauna yankin sun nemi agaji yayin da 'yan bindiga suka fara taruwa domin kai harin amma ba a kawo musu dauki ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya jawo martani daga jama’a da dama, ciki har da ‘yan uwa da abokansa da ke nuna damuwa da addu’a kan lamarin.
Yadda aka sace Manjo Janar Maharazu Tsiga
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa kafin harin, jama’a sun lura da taruwar wasu mutane da ake zargin ‘yan ta’adda ne a kusa da garin.
Wani mazaunin garin ya ce:
"Mun ga ‘yan bindiga sama da 100 sun taru a kusa da yankin. Mun yi kira ga jami’an tsaro amma babu wanda ya zo har sai da abin da muke tsoro ya faru,"
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kutsa cikin yankin a kan babura, inda suka yi awon gaba da mutane 11, sai dai daga baya uku sun tsere.

Kara karanta wannan
"Ba za mu bari ba," Lauya, Abba Hikima ya je inda ake harbe mutane wajen rusau a Kano
An sace mutane bakwai daga garin Tsiga, yayin da aka dauke wasu biyu daga wasu ƙauyuka da ke kusa.
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
Duk da yadda lamarin ke tayar da hankali, har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ba ta fitar da wata sanarwa kan batun ba.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa har yanzu suna jiran cikakken bayani kan sace tsohon babban daraktan na NYSC.
"Mun samu rahoton amma ba mu da cikakken bayani a halin yanzu. Idan mun kammala bincike, za mu fitar da sanarwa,"
- DSP Abubakar Sadiq
Martanin jama'a kan sace Janar Tsiga
Bayan faruwar lamarin, mutane da dama sun nuna fargaba da yadda matsalar garkuwa da mutane ke ƙara tsananta a jihar Katsina da ma Najeriya baki ɗaya.
A shafukan sada zumunta, wasu mutane sun nuna tausayi ga Manjo Janar Tsiga da iyalansa, tare da yin addu’ar Allah SWT ya kubutar da shi.

Kara karanta wannan
Barazanar tsaro: An kama 'yan kasashen waje 165 da shirin kulla makirci a Najeriya
Wasu kuwa sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su gaggauta kawo karshen irin wannan matsala da ke barazana ga rayuwar al’umma.
An samu dan firamare da bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa an samu wani yaro dan firamare a jihar Akwa Ibom da ke Kudancin Najeriya dauke da bindiga a makaranta.
Rahotanni sun nuna cewa jami'an 'yan sanda sun kama mahaifin yaron bayan ya tabbatar da cewa a dakin babansu ya samu bindigar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng