Bayan Nanata Binani Ta Lashe Zabe, INEC Ta Yi Martani ga Kalaman Hudu Ari

Bayan Nanata Binani Ta Lashe Zabe, INEC Ta Yi Martani ga Kalaman Hudu Ari

  • Hukumar INEC ta mayar da martani kan zarge-zargen da korarren kwamishinan zaben Adamawa, Hudu Yunusa-Ari ya yi
  • Hukumar ta bukaci tsohon kwamishinan zaben ya kare kansa a kotu ba kame-kame ba da gudanar da hira da manema labarai
  • Yunusa-Ari ya ce ba a ba shi damar kare kansa ba, amma INEC ta ce dole ne ya bi doka don kare mutuncinsa ba kafar sada zumunta ba
  • Tsohon kwamishinan ya sake tabbatar da cewa yar takarar gwamna a APC, Sanata Aishatu Binani ce ta lashe zaben Adamawa a 2023

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bukaci Hudu Yunusa-Ari, tsohon kwamishinan zabe na Adamawa, da ya kare kansa a kotu.

Hukumar ta ce bai kamata Hudu Ari ya yi ta taron manema labarai ba da zarge-zarge, madadin haka, ya je kotu ya kare kansa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Gombe ta fusata, an ba da umarnin farauto makasan malamin addini

INEC ta caccaki tsohon kwamishinan zabe a Adamawa
Hukumar INEC ta bukaci Hudu Ari ya kare kansa a kotu madadin hira da yan jaridu. Hoto: INEC Nigeria.
Asali: Facebook

Hudu Ari ya dage cewa Binani ta lashe zabe

A wata hira da The Nation ta samu, mai magana da yawun shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi ya ce hukumar ba za ta yi tsokaci kan karar da ke kotu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Asabar 8 ga watan Janairun 2025, Hudu Yunusa-Ari ya yi taron manema labarai, yana mai cewa INEC ba ta ba shi damar kare kansa ba.

Tsohon kwamishinan zaben ya nace kan cewa Binani ce ta lashe zaben gwamna na Adamawa a 2023 wanda hakan ya jawo martanin al'umma.

INEC ta kalubalanci Hudu Ari kan kalamansa

Da yake mayar da martani, Oyekanmi ya ce tunda Yunusa-Ari ya dawo gida, zai iya kare kansa a kotu.

"Ina amsa tambayarku, mun samu labarin hira da tsohon kwamishinan zaben Adamawa, Yunusa-Ari, ba wata sabuwar magana a abin da ya fada."
"A karshe dai, kotu ce ta yanke hukunci a kan zaben Adamawa tun daga matakin kotun sauraron kararrakin zabe har zuwa kotun koli."

Kara karanta wannan

Tirkashi: An maka Shugaba Tinubu a kotu kan badakalar kwangilar Naira biliyan 167

"Hukumar ba za ta yi tsokaci kan abin da ya aikata ba, tun da maganar tana kotu, kuma yana da damar kare kansa a gaban shari’a."

- Rotimi Oyekanmi

Majalisa ta amince da korar Hudu Ari

Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta amince da bukatar shugaba Bola Tinubu na tsige kwamishinonin hukumar zaɓe ta ƙasa watau REC na jihohi uku.

Hudu Ari, kwamishinan zaɓen Adamawa wanda ya ayyana Aishatu Binani a matsayin wacce ta samu nasara a zaben gwamna na cikin waɗanda aka kora.

Shugaban ƙasa ya nemi korar kwamishinonin hukumar ta INEC ne sakamakon laifuffukan da suka aikata tun a lokacin babban zaɓen 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.