Tirkashi: An Maka Shugaba Tinubu a Kotu kan Badakalar Kwangilar Naira Biliyan 167

Tirkashi: An Maka Shugaba Tinubu a Kotu kan Badakalar Kwangilar Naira Biliyan 167

  • SERAP ta maka Shugaba Bola Tinubu a kotu kan zargin rashin binciken kwangilolin da ba a aiwatar da su ba da suka lakume N167bn
  • SERAP ta bukaci a bayyana sunayen kamfanonin da aka ba kwangilolin are da gurfanar da su don dawo da kudaden jama'a da aka ba su
  • Kungiyar ta ce rashin daukar mataki ya yi tasiri wajen rage ingancin ayyukan gwamnati kuma ya saba wa Kundin Tsarin Mulki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - SERAP ta maka Shugaba Bola Tinubu a kotu saboda gazawar gwamnatinsa na gurfanar da 'yan kwangilar da suka karɓi N167bn ba tare da yin aikin ba.

SERAP ta shigar da ƙarar ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, ƙarƙashin lamba FHC/L/MISC/121/2025, inda ta haɗa ministan shari’a, Lateef Fagbemi.

Kara karanta wannan

'Ka taka masa birki': An kai karar El Rufai gaban Nuhu Ribadu, an hango hatsarin kalamansa

SERAP ta gabatar da bukata gaban kotu yayin da ta gurfanar da Shugaba Tinubu
SERAP ta maka Tinubu a kotu kan kwangilolin N167bn da ba a aiwatar ba. Hoto: @SERAPNigeria, @officialABAT
Asali: Twitter

SERAP ta maka Tinubu a gaban kotu

A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, SERAP ta roki kotun ta tilasta wa Tinubu umartar ministan kudi, Olawale Edun, ya bayyana sunayen kamfanonin da aka ba kwangilolin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SERAP ta bukaci kotu ta umarci gwamnati ta gurfanar da waɗanda abin ya shafa tare da dawo da dukiyar da aka yi asararta saboda gaza aiwatar da ayyukan.

Bugu da ƙari, kungiyar ta buƙaci ministan kudi ya bayyana sunayen masu hannun jarin kamfanonin da suka karɓi kuɗin da cikakkun bayani kan kwangilolin da aka ba su.

Sunayen wasu hukumomi da badakalar ta shafa

SERAP ta bayyana cewa buƙatun nata sun ta’allaka ne kan rahoton 2021 na babban mai binciken kuɗi na tarayya wanda ya gano wasu ayyukan da aka yi watsi da su.

A rahoton, an bayyana cewa hukumar kasuwancin lantarkin Najeriya (NBET) ta biya Naira biliyan 100 na kwangilolin da ba a kammala ba.

Kara karanta wannan

"Shirin gwamnati ya gaza, " Tsohon gwamnan APC ya fito da matsalolin mulkin Tinubu

Sauran hukumomin da ake zargin an tafka badakalar sun haɗa da NCS, NPC, PTDF da sauransu, kamar yadda rahoton Premium Times ya nuna.

SERAP ta fadi illar rashin binciken kwangilolin

SERAP ta yi ikirarin cewa rashin daukar mataki kan waɗannan zarge-zargen ya yi tasiri wajen lalata shugabanci da kuma rage ingancin ayyukan gwamnati.

Kungiyar ta ce hukunta waɗanda suka aikata laifin zai taimaka wajen magance almubazzaranci da cin hanci a hukumomin gwamnati.

SERAP ta ƙara da cewa zarge-zargen sun saba wa Kundin Tsarin Mulki na Najeriya, dokokin cin hanci na ƙasa, da kuma yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan cin hanci.

SERAP ta garzaya kotu kan karin kudin sadarwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, SERAP ta maka gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) a kotu kan karin kudin kira da data.

SERAP ta ce karin kudin da kamfanonin sadarwa za su yi da ya kai kashi 50% ya sabawa ka'ida, kuma ya saba wa dokokin kasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.