'Binani Ce Ta Ci Zaɓen Adamawa': Hudu Ari Ya Yi Rantsuwa an Tilasta Shi game da Fintiri
- Tsohon kwamishinan INEC a jihar Adamawa, Hudu Ari, ya jaddada cewa Sanata Aisha Binani ta lashe zaben gwamna a 2023
- Hudu Ari ya ce yana da hujjojin takardu da ke nuna Binani ta doke Gwamna Ahmadu Fintiri, amma INEC da kotun zabe sun yi watsi da su
- Ya rantse da Al-Qur'ani cewa ana matsa masa lamba ya ayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zabe, in ba haka ba, ba za a kare shi ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Bauchi - Kwanaki bayan majalisar dokoki ta amince da korarsa daga aikin INEC, tsohon kwamishinan zabe na Adamawa, Barr Hudu Ari ya magantu.
Hudu Ari ya dage cewa ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC, Sanata Aisha Binani, ita ce ta lashe zaben gwamna na 2023 duk da ce-ce-ku-ce da aka yi.

Kara karanta wannan
'Shi zai iya gyara Najeriya': Dan PDP ya roki Kwankwaso, Obi su hade da Atiku Abubakar

Asali: Twitter
Waye ya ci zaɓen jihar Adamawa a 2023?
Hudu Ari, wanda aka kora daga aiki kwanan nan, ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Bauchi, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon kwamishinan ya kare kansa kan dalilan da suka sa ya sanar da sakamakon zaben shekarar 2023 a Adamawa.
Ari, wanda ya nuna bacin ransa, ya jaddada cewa yana da duk wasu takardu da ke tabbatar da cewa Binani ta kayar da Gwamna Ahmadu Fintiri na PDP a zaben.
Ya ce Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu da kuma kotun zabe, sun yi watsi da hujjojin da ya gabatar dangane da magudin da aka yi a zaben gwamna mai cike da rikici, TheCable ta ruwaito.
Barazanar da aka yi wa Hudu Ari a Adamawa
A yayin da yake rike da Al-Qur’ani, Ari ya yi rantsuwa an yi masa barazana kan cewa dole ne ya bayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zabe, in ba haka ba ba za a kare rayuwarsa ba.
“Na gano cewa Shugaban Sashen ICT, Bala Aji, bai gudanar da aikinsa kamar yadda ya kamata ba a lokacin zabe, ya mika wasu takardu na zabe har guda 20,000 ga gwamnan Adamawa.”
“Ni da kwamishinan ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro muka sami rahoto kan hakan, mun je gidan sirrin gwamnan, inda muka iske Sakataren Gwamnati da wasu jami’an gwamnati suna aiki da takardun zaben.”
“Mun same su suna amfani da wadannan takardu a fili, mun rubuta rahoto kan abin da ke faruwa, ba wannan kadai ba, Bala Aji ya karkatar da wasu daga cikin takardunmu.”
- Hudu Ari
Hudu Ari ya yi tone-tone kan zabe
Tsohon kwamishinan ya kara da cewa:
“Ya kamata INEC ta dauki mataki kan sayen kuri’u, sun san abin da ke faruwa amma ba su yi komai ba.”
“Abin da na rubuta wa hedikwatar INEC an ajiye shi gefe, wannan yana daga cikin abubuwan da ba zan taba mantawa da su ba.”

Kara karanta wannan
'Ba ni da hannu a ciki, Tsohon gwamna ya musanta zargin kisan tsohon minista a Najeriya
Hudu Ari ya ce ba a ba shi damar kare kansa ba, kuma kotun zabe da hukumar INEC sun yi watsi da dukkan hujjojinsa kan dalilin da ya sa ya ayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zabe.
Majalisa ta amince da korar kwamishinan INEC
Kun labarin cewa Majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaba Bola Tinubu na tsige kwamishinonin hukumar zaɓe ta ƙasa watau REC na jihohi uku.
Hudu Ari, kwamishinan zaɓen Adamawa wanda ya ayyana Aishatu Binani a matsayin wacce ta samu nasara na cikin waɗanda aka kora.
Asali: Legit.ng