Gwamnatin Gombe Ta Fusata, An ba da Umarnin Farauto Makasan Malamin Addini
- Gwamnan Gombe ya yi Allah-wadai da kisan Fasto Bala Galadima, jagoran cocin ECWA Lubo da ake zargin 'yan fashi ne su ka kai masa hari
- Gwamna Mohammed Inuwa Yahaya ya umarci hukumomin tsaro da su yi bakin kokarinsu wajen kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki
- Ya kwantar da hankalin jama'ar jiharsa, inda ya tabbatar masu cewa za a dauki matakan tsaro masu karfi don kare rayuka da dukiyoyinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Gombe - Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi Allah-wadai da kisan Fasto Bala Galadima.
Kafin kisansa, Fasto Galadima ya kasance jagoran coci a Evangelical Church Winning All (ECWA) da ke garin Lubo a karamar hukumar Yamaltu/Deba.

Asali: Facebook
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama’a na Gwamnatin Jihar Gombe, Ismaila Misilli, ya fitar a ranar Litinin, wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yahaya ya bayyana kisan a matsayin mummunar ta’asa da ke barazana ga zaman lafiyar jihar Gombe, wacce ta dade tana zaune a cikin kwanciyar hankali.
Gwamna ya ba da umarnin kamo makasan fasto
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an kashe Rabaran Galadima a daren Lahadi a gidansa da ke Lubo, ana zargin wasu ‘yan fashi da makami suka kai masa hari.
Gwamnan ya jaddada cewa irin wadannan laifuffuka ba za su hana zaman lafiya da hadin kai a jihar ba, domin za a yi fito-na-fito da ta'addancin.
Ya ce:
"Ba za mu bari miyagu su lalata zaman lafiya da tsaron jiharmu ba. Na umarci hukumomin tsaro da su yi bakin kokarinsu wajen kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da gurfanar da su a gaban shari’a."
Gwamna ya sha alwashin magance rashin tsaro
Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, ya tabbatar wa al’ummar jiharsa cewa za a ci gaba da daukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyinsu.
Ya kara da cewa:
"Ina tabbatar wa mutanen Gombe cewa gwamnati za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro.
"Za mu dauki kwararan matakai tare da amfani da karfin da ya dace domin kawar da miyagun da ke fakewa a ko’ na."
'Yan ta'adda sun kashe malamin addini a Gombe
A abaya, mun ruwaito cewa wasu ƴan bindiga da ake zaton ƴan fashi da makami ne sun kashe wani malamin addinin Kirista, Rabaran Bala Galadima, a garin Labo da ke jihar Gombe.
Jami'in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da cewa 'yan bindigan sun kai wa malamin hari cikin ƙaramar hukumar Yamaltu-Deba ta jihar Gombe, a daren ranar Lahadi.
Kafin mutuwarsa, Rabaran Bala Galadima ya kasance babban mai wa’azi a cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) da ke garin Lubo, kuma yanzu haka an shiga farautar wadanda su ka kashe shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng