Yawan Yin Jima'i na Hana Kamuwa da Sankarar Mafitsara ga Maza? Likita Ya Magantu
- Dakta Sam Adegboye na asibitin FETHI ya musanta ikirarin cewa yawan jima’i na rage hadarin kamuwa da sankarar mafitsara
- Likitan ya ce akwai bukatar maza su yi gwajin PSA domin sanin lafiyar mafitsararsu, don kar a kamu da BPH, a dauka sankara ce
- Ya yi gargadi kan cewa ana iya samun rashin tabbas a sakamakon gwajin PSA idan namiji ya yi jima’i ko motsa jiki kafin gwajin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Wani likita, Dakta Sam Adegboye, ya musanta ikirarin cewa yawan yin jima'i na rage hadarin kamuwa da cutar sankarar mafitsara ga maza.
Adegboye shi ne mataimakin babban jami’in lafiya kuma likita a asibitin koyarwa na tarayya da ke Ido-Ekiti, jihar Ekiti.

Asali: UGC
Yawan jima'i na kwantar da kansar maraina?
Likitan ya musanta wannan ikirari a wata hira ta waya da ya yi da hukumar dillancin labarai na Najeriya (NAN) a garin Osogbo, babban birnin jihar Osun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakta Adegboye ya ce:
“Yawancin mujallun kiwon lafiya ba su goyi bayan wannan ra’ayi ba. Mun yi nazari a mujallar lafiya ta Amurka, kuma mun gano gano rashin tabbas a wannan ikirarin.”
A cewar Dakta Adegboye, binciken kimiyya kan alakar jima'i da sankarar mafitsara yana buƙatar tabbaci na gaskiya kuma ya dogara ne da shaidun kwararrun masana.
An shawarci maza su yi gwajin lafiyar maraina
Likitan ya ce:
“Babu kwararan hujjoji daga masana kimiyya da ke goyon bayan wannan ra’ayi, ko da yake wasu masu ra’ayin gargajiya na iya amincewa da shi.”
Ya kara da cewa akwai gwajin sankarar mafitsara (PSA) wanda maza za su iya yi don bincikar halin lafiyar 'ya'yan marainansu.
Dakta Adegboye ya ce akwai lalurar BPH da ke kama mafitsara amma ba kansa ba ce, wadda kan haddasa matsalolin fitsari musamman ga mazan da suka tsufa.
“BPH ba yana nufin sankarar mafitsara ba, amma yana jawo girman maraina wanda kuma ba ya da alaƙa da cutar sankarar."
- Dakta Adegboye.
'A guji yarda da ra'ayoyi marasa tushe' - Likita
The Nation ta rahoto Dakta Adegboye ya ce:
“Idan girman maraina ya karu, yana shafar bututun fitsari (urethra), wanda ke sanya wahalar fitsari. Likita kan sanya robar catheter don taimaka wajen fitar da fitsarin.”
Dakta Adegboye ya kuma yi karin haske kan cewa idan PSA ya nuna karuwar kwayoyin hormone, hakan ba lallai ya nufin kamuwa da cutar mafitsara ba.
Ya yi gargadin cewa:
“Idan mutum ya yi jima’i kwanaki biyu kafin gwajin PSA, ko ya motsa jiki sosai, za a iya samun sakamako marar tabbas, don haka a kauracewa yin hakan."
A karshe, ya yi kira ga maza da su rika yin gwajin PSA don gano lafiyar mafitsararsu, sannan su kuji yarda da ra’ayoyi marasa tushe wajen yanke hukunci kan lafiyarsu.
An yiwa sarkin Saudiya tiyata a mafitsara
A wani labarin, mun ruwaito cewa an yi nasarar yi wa Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz, tiyata a mafitsara a asibitin King Faisal da ke Riyadh.
Sarki Salman zai ci gaba da jinya a asibitin na kwanaki kamar yadda likitoci suka bada shawara domin ya samu ya murmure.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng