Gwamnatin Jihar Kano Ta Runtuma Kora a Ma'aikatar Shari'a, An Samu Karin Bayani
- Hukumar shari’ar Kano ta kori ma’aikata biyu bayan sun amsa laifin karɓar rashawar N214,000 daga wani Alhaji Sani Rimin Gado
- Gwamnatin jihar ta yi wa Hudu Idris ritayar dole tare da rage masa matsayi, yayin da aka sallami Abba Bala Gwarzo daga aiki kai tsaye
- Hukumar ta kuma janye dakatarwa da aka yi wa wasu ma’aikata uku, saboda rashin hujja kan zarge-zargen da aka yi masu a baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Hukumar shari’a ta jihar Kano (JSC) ta kori wani ma’aikaci tare da tilasta wani ya yi ritaya saboda karɓar cin hanci.
Kakakin hukumar JSC, Baba Jibo, ya fitar da sanarwa ranar Lahadi, inda ya ce an yanke hukuncin ne a taron hukumar karo na 79.

Asali: Twitter
Sanarwar ta ce an gudanar da taron ne a ranar 6 ga Fabrairu, ƙarƙashin jagorancin shugabar alkalan Kano, Mai shari’a Dije Aboki, inji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An sallami ma'aikatan shari'a a Kano
Wani Alhaji Sani Bozo Rimin Gado ne ya kai ƙorafin cewa Hudu Idris da Abba Bala na babbar kotun shari’a ta Gwarzo sun nemi kuɗi ba bisa ƙa'ida ba.
Bayan bincike, an gano cewa ma’aikatan sun karɓi cin hancin N214,000 daga hannun Alhaji Sani, kuma sun amsa laifinsu a gaban kwamitin JPCC.
Hukumar ta ɗauki matakin ritayar dole kan Hudu Idris tare da rage masa matsayi, yayin da aka kori Abba Bala daga aiki, bisa sahalewar shugabar alkalan jihar.
An wanke wasu ma'aikata 3 daga zargi
Sanarwar ta tabbatar cewa matakan sun yi daidai da kokarin hukumar wajen tabbatar da gaskiya da amana a fannin shari’a.
Mista Jibo ya ce hukumar ta janye dakatarwar da aka yi wa wasu ma’aikata guda uku da aka zarga da laifin rubuta jabun umarnin kotu.
Ya ce an wanke Bilya Abdullahi, Auwalu Khalil da Ismaila Garba saboda babu hujjar tabbatar da zargin da aka yi musu.

Kara karanta wannan
'Diyar Ganduje ta samu babban mukamin gwamnati, majalisa ta aika sunaye ga Tinubu
Majalisa ta amince da nadin Dije Aboki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar dokokin Kano ta amince da naɗin Mai shari’a Dije Aboki a matsayin shugabar alkalan jihar.
Kakakin majalisar Kano, Ismail Falgore, ya karanta wasiƙar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike wa majalisar na naman amincewa da nadin Dije.
Haka kuma, majalisar ta amince da naɗin kwamishinoni uku — Ibrahim Fagge, Ibrahim Namadi, da Amina Abdullahi-Sani.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng