Ya kamata ko wani namiji yayi jima'i akalla sau 21 a wata, Sabon Bincike

Ya kamata ko wani namiji yayi jima'i akalla sau 21 a wata, Sabon Bincike

  • Masana sun yi alhinin yawaitar cutar dajin mafitsara cikin mazaje masu shekaru 40 da abinda yayi sama
  • Bincike na gudana kan yadda za'a magance wannan cutar cikin mazaje masu yawan shekaru
  • Binciken Jami'ar Harvard ya alakanta yawan yin jima'i da raguwar kamuwa da cutar

Wani sabon bincike ya nuna cewa ya kamata kowani namiji yayi inzali akalla sau 21 a wata domin kariya daga cutar dajin mafitsara da ke yawaita cikin maza.

A cewar masu bincike a Jami'ar Harvard dake Amurka, an gudanar da wannan bincike ne kan maza 31,925.

Binciken wanda aka wallafa a mujallar Ilimi ta European Urology, mazaje 31,925 sun bayyana adadin lokutan da suke inzali a wata.

Daga wannan bincike, masanan sun gano cewa yawan inzali na rage yiwuwar kamuwa da cutar dajin mafitsara da kashi uku.

Kara karanta wannan

Rikici: An farmaki hadimin Ganduje a Kano, ya ce 'yan Kwankwasiyya ne suka sace wayarsa

Mawallafan suka ce:

"Mun yi bincike kan shin yawan inzali lokacin da mutum ke girma na da alaka da kamuwa da cutar daji cikin mazaje a Amurka."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun gano cewa akwai raguwar yiwuwar kamuwa da cutar 'Kansa' cikin mazajen da suka fada mana suna inzali sosai lokacin da suke girma fiye da wadanda ba suyi sosai."

Ya kamata ko wani namiji yayi jima'i akalla sau 21 a wata, Sabon Bincike
Ya kamata ko wani namiji yayi jima'i akalla sau 21 a wata, Sabon Bincike

Asali: Legit.ng

Online view pixel