'Najeriya Ta Rasa Aboki': An Shiga Jimami da Tsohon Shugaban Kasa Ya Kwanta Dama
- Sam Nujoma, jagoran juyin juya hali kuma shugaban kasar Namibia na farko, ya rasu yana da shekara 95, in ji fadar shugaban kasa
- Ya taka rawar gani wajen kwatar wa Namibia ’yanci daga Afrika ta Kudu, inda aka tabbatar da shi a matsayin "Uban Gidan Namibia" a 2005
- Sanata Shehu Sani ya ce Najeriya ta yi rashin aboki na gaskiya, wanda ya nuna godiya ga gudunmawar da aka ba shi lokacin neman ’yanci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Namibia - Sam Nujoma, fitaccen dan gwagwarmaya kuma jagoran yakin guerilla, ya rasu yana da shekara 95, inji fadar shugaban kasar Namibia a Lahadi.
Nujoma ya zama zababben shugaban kasar Namibia na farko bayan ya jagoranci samun ‘yancin kai daga Afrika ta Kudu a ranar 21 ga Maris, 1990.

Asali: Twitter
Nujoma ya kwatowa kasar Namibia 'yanci
Ya taka rawar gani a gwagwarmayar samun ‘yanci, inda ya zama alamar juriyar Namibiyawa da burinsu na ganin adalci da zaman lafiya mai dorewa, inji rahoton Reuters.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A shekarar 2005, majalisar dokokin kasar ta tabbatar da shi a hukumance a matsayin "Uban Gidan kasar Namibia" saboda irin gudunmawar da ya bayar.
Duk da haka, shugabancinsa ya gamu da suka saboda tsaurin ra’ayi kan kafofin watsa labarai da matsayinsa kan batun luwadi da madigo.
Gwamnati ta sanar da rasuwar Nujoma
Nujoma ya kasance mai marawa shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe, baya kan karbe gonaki daga fararen fata, amma a kasarsa yana bin tsarin saye da sayarwa.
"Tushen kafuwar Jamhuriyar Namibia ya girgiza," a cewar fadar shugaban kasa, a sakon ta'aziyya da ya wallafa a shafinta na X.
Fadar shugaban kasar ta ce Nujoma ya kwanta jinya na makonni uku, amma a wannan karon, bai iya tashi daga cutar da ta kama shi ba.

Kara karanta wannan
'Ka taka masa birki': An kai karar El Rufai gaban Nuhu Ribadu, an hango hatsarin kalamansa
'Najeriya ta rasa aboki' - Shehu Sani
Sanata Shehu Sani ya yi alhinin rasuwar Najuma yana mai cewa Najeriya ta rasa "aboki na gaskiya wanda ya ziyarce ta a lokuta da dama."
Shehu Sani ya ce tsohon shugaban kasar ya sha ziyartar Najeriya domin nuna godiya ga gudunmawar da aka bashi lokacin neman 'yancin Namibiya.
"Na samu labarin rasuwar tsohon shugaban Namibia, Kwamred Sam Najuma. Afrika ta yi rashin babban dan gwagwarmaya da ya yi fadi tashi don kwato wa kasarsa 'yanci."
- A cewar Shehu Sani, a sakon da ya wallafa a shafinsa na X.
Shugaban kasar Namibia ya rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban ƙasar Namibia, Hage Geingob, ya rasu a safiyar Lahadi, 4 ga Fabrairun 2024, yana da shekaru 82, in ji fadar shugaban ƙasa.
Mataimakin shugaban ƙasa, Nangolo Mbumba, zai jagoranci jihar a matsayin rikon kwarya har zuwa lokacin da za a gudanar da zaben ƙasa.
Za a gudanar da zaben shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokoki kafin ƙarshen wannan shekara, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Asali: Legit.ng