Tabdijan:Tabdijan: Mafi yawancin Mutane basu san haka rikon fitsari ke da illa ga Mutum ba
- Mai dabi'ar matse fitsari yana cikin matsala
- Matsalar ba ta tsaya kan yin fitsari a wando kawai ba, har ta kai ga lalata wasu sassan jiki
- Amma masana sun bayar da shawarar yadda zabi don matse fitsarin na dan wani lokaci
riƙon fitsari ba sabon abu ba ne ga mata ko maza, yara ko manya, hasali ma abu ne da ya zama ruwan dare.
Shin ko kunsan cewa mafitsarar babban mutum na iya ajiyar fitsarin da yawansa bai wuce babban kofi biyu ne na ruwa ba kacal? Kuma da zarar ya haura hakan, zaka fara jin mutane na cewa fitsari ya matse ni.
Kunga kenan. zaku iya auna yawan adadin ruwa ko lemon da zaku sha idan zaku je wurin da babu makewayi.
Ko kun taɓa tambayar kanku cewa ko riƙon fitsarin da kuke yi na da wata illa ga lafiyarku?
A yau Legit.ng ta kawo muku jerengiyar bayanai kan rike fitsarin da maza da mata kanyi a lokuta daban-daban bisa dalilai mabambamta.
Duk da dai babu wata doka da ta nuna lallai-lallai ga lokutan da Mutum zai yi fitsari, amma yinsa da wuri ko akasin hakan ya ta'allaƙa ne ga yanayin halitta, kowa da kalar tasa.
Idan har Mutum na da sakakkiyar mara, da rike fitsari ke masa wahala to riƙon nasa bai wuce ace kamar ƙoƙarin horas da marar ne ba.
Amma a wasu lokutan riƙon fitsarin kan zama illa ga lafiya da kuma hadarin kamuwa da ciwon ƙoda, idan har kana da ɗaya daga cikin abubuwan da zamu lissafa a ƙasa:
Toshewa ko sirancewar bututun fitar fitsari
Kakkatsewar fitowar fitsari
Matsalar koda
Raguwar fitsari a cikin mara
Mata masu ciki na cikin babban haɗari mutuƙa, ga ciki ga kuma riƙon fitsari wanda na iya jawo ƙaruwar haɗarin kamuwa da wasu cututtukan.
KU KARANTA: Wuraren tarihi 13 masu muhimmanci a garin Makkah
To amma me yake faruwa da jikan Mutum idan ya riƙe fitsari?
Bayanin dalilin da yasa Mutum yake jin fitsari ya wuce kawai don mara ta cika ne, abu ne mai wahalar ganewa, amma daga cikin abubuwan da suke faruwa ya haɗa da; wasu sassan jiki da gaɓoɓi tare da aiki da kwakwalwa sannan sai kaji cewa lokaci yayi na ayi fitsari.
Ga wasu matan yawaitar saurin yin fitsarinsu na ƙaruwa bayan sun fara haihuwa, wannan na faruwa ne sakamakon sauye-sauyen da halittun jikin nasu suka samu, ga kuma rauni da gaɓoɓin jikin suka yi.
Wasu kuma koda maza ne, idan girma ya fara kama su, gaɓɓansu musamman mafitsara kan fara ƙirƙirar halayyar saurin fitar da abinda ke cikin mara sakamakon ɓacin rai ko mummunar fusata.
Abu mai muhimmanci gaske da ya kamata mutum ya sani shi ne, mutukar yana yawaita riƙe fitsari ba tare da zubar da shi ba akai-akai, to babu shakka yana cikin babban haɗarin kamuwa da cututtukan dake da alaƙa da mafitsara (UTI).
Wani abin lura kuma shi ne, ba rashin yin fitsari ne kawai ke iya haifar da matsalar mafitsarar ba; hatta rashin shan isasshen ruwa kan iya haddasa matsalar ta UTI, sakamakon babu isasshen fitsari a cikin marar da kwakwalwa zata karbi saƙon cewa lokacin fitsari yayi. A dalilin haka kuma sai a samu matsalar bayar da umarni da kuma sanin lokacin cewa fitsari yayi.
Ga wasu alamomi da ya kamata a lura da su sosai, matukar ana fuskantarsu to wataƙila an yi arangama da matsalar ciwon mafitsara (UTI). Kuma lokaci yayi na zuwa ziyarci likita.
Daga cikin alamomin akwai:
Yawaitar jin fitsari
Jin zafi yayin fitsari
Yin fitsari nai war
Canzawar kalar fitsari kamar kalar hadari
Fotowar jini tare da fitsarin
Jin raɗaɗi yayin fitsari
Mafitsara na daya daga cikin sassan jikn dake taimakawa Mutum yin fitsari bayan koda ta tace ruwan da take bukata, a wasu lokutan, akan samu yanayin da fitsarin zai koma inda ya fito wato hanyar koda wanda kuma hakan babbar matsala ce.
maganar gaaskiya ita ce, maza garzaya kayi fitsari da zarar kaji bukatar hakan, kar kace har sai ya matseka balle ka rika matse shi har ya haifar maka da matsala.
Amma idan babu makewayi kusa ko baka son fita daga inda kake, ga wasu yan dabaru da zaku amfani dasu da zasu ara muku lokaci kafin a samu zarafin yinsa.
daga cikin abubuwan dabaru da zaku iya yi wajen rike fitsari yayin da ya matseku akwai:
Sauraren waka musamman idan da bututun sautin kunne
Cigaba da zama idan dama a zaune kake
Karatun littafi
Cigaba da duba sabbin labarai a shafukan sada zumunta ko wasa (Game)
Samun dimi ko kin zuwa waje mai sanyi
zuwa ganin likita shi ne babbar dabara yayin da kake zargin kamuwa da cututtuka domin duba lafiyarka.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku
ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng