An samu nasarar yi wa Sarki Salman tiyata a mafitsara

An samu nasarar yi wa Sarki Salman tiyata a mafitsara

Saudi Gazette ta ruwaito cewa, an samu nasarar yi wa Sarki Salman Bin Abdulaziz na kasar Saudiya tiyata a mafitsara a babban asibitin King Faisal da ke birnin Riyadh.

Kamfanin dillancin labarai na kasar SPA a ranar Alhamis ya ruwaito cewa, Sarki Salman zai ci gaba da kasancewa a asibitin har zuwa wasu kwanaki domin ci gaba da duban lafiyarsa kamar yadda likitocinsa suka ba da shawara.

Majibincin Masallatan Harami biyu na kasar, ya nuna godiyarsa ga duk wadanda suka kira ko aiko masa da sakon fatan alheri.

Babu shakka shugabannin kasashen duniya da dama sun rika aike wa da Sarkin sako na fatan samun waraka cikin gaggawa, ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Wannan sako yana kunshe cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya sanya wa hannu kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Sarki Salman Bin Abdul'aziz
Hoto daga jaridar Daily Nigerian
Sarki Salman Bin Abdul'aziz Hoto daga jaridar Daily Nigerian
Asali: Twitter

Shugaban ya ce: "A madadi na, gwamnati da jama'ar Najeriya, ina yin addu'ar fatan alheri da kuma samun sauki ga Sarkin Saudiyya, daya daga cikin mafi kyawun shugabannin da na taba haduwa da su a yayin mu'amala da shugabannin duniya."

"Sarki Salman aboki ne na kwarai wanda ya bai gaza wajen tabbatar da Najeriya a kowane lokaci ta hanyar hadin gwiwa da aiki tare."

"A yayin da Sarkin yake samun kulawa a asibiti, ina masa fatan alheri da addu'o'in samun lafiya cikin gaggawa."

A makon da muke ciki ne Legit.ng ta ruwaito cewa, an kwantar da Sarki Salman a asibiti sakamakon larura da ya samu a mafitsararsa.

Rahotannin da su ka fito daga gidajen jaridun kasar a ranar Litinin, sun tabbatar da cewa an kwantar da sarkin mai shekaru 84 a asibiti.

SPA, Kamfanin dillacin labarai na kasar ya bayyana cewa an dai kwantar da Salman Bin Abdul'aziz ne a wani asibiti da ke babban birnin Riyadh.

KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun saki fursunoni a Barikin Ladi

Bayan rahotannin da suka bayyana cewa Sarki Salman ya na fama da kumburi a mafitsararsa, babu wani labari da aka samu game da halin Basaraken.

An ruwaito cewa ana yi wa Sarkin na Saudiya, kuma mai kula da masallatan alfarma masu tsarki da ke biranen Makkah da Madina, gwaje-gwaje a asibitin.

Dattijon Sarkin ya yi shekaru biyar ya na mulki, amma ana ganin babban ‘dansa kuma Yarima mai jiran gado watau Muhammad Bin Salman, shine ya ke jan ragamar kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel