Luguden Sojoji: Manyan Ƴan Ta'adda da Mayaƙa Sama da 30 Sun Baƙunci Lahira a Arewa

Luguden Sojoji: Manyan Ƴan Ta'adda da Mayaƙa Sama da 30 Sun Baƙunci Lahira a Arewa

  • Sojojin saman Najeriya sun yi nasarar kashe manyan kwamandojin ISWAP da wasu mayaƙansu a jihar Borno
  • Kakakin rundunar NAF, AVM Edward Gabwet ya ce wannan samamen ya lalata muhimman kayayyakin ƴan ta'addan a gabar tafkin Chadi
  • A cewarsa, wannan wata alama ce da ke nuna sojoji sun shirya kawo karshen ta'addanci a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Dakarun sojojin sama na rundunar Operation Hadarin Kai (OPHK) sun kai samame ta sama kan mafakar ƴan ta'addan ƙungiyar ISWAP a jihar Borno.

Yayin wannan farmaki, jirgin yaƙin sojojin ya samu nasarar hallaka ƴan ta'adda aƙalla 30 a yankin kauyen Kolleram da ke gabar Tafkin Chadi.

Jirgin sojoji.
Luguden NAF ya yi ajalin manyan ƴan ta'adda a Borno Hoto: Nigeira Air Force
Asali: Facebook

Wannan nasara na ƙunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojojin saman Najeriya, AVM Edward Gabkwet, ya fitar ranar Talata a Abuja, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna Malam El-Rufa'i ya bayyana babbar matsala 1 tak da ta addabi Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce farmakin da jirgin sojojin ya kaddamar kan ƴan ta'adda ranar 13 ga watan Afrilu, ya masu gagarumar ɓarna da kuma rage mugayen iri a Arewa maso Gabas.

Kakakin NAF ya ce an samu gagarumar nasara a samamen saboda bincike bayan farmakin ya nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda sama da 30.

An kashe manyan kwamandoji

Gabkwet ya ce daga cikin wadanda aka kashe akwai wasu manyan kwamandojin ‘yan ta’addan da suka hada da Ali Dawud, Bakura Fallujah, da kuma Malam Ari.

"Bugu da kari, an lalata motoci da dama, babura, da sauran kayan aikin da suke amfani da su, wanda hakan ya kawo cikas ga ayyukan 'yan ta'addan.
"Bayanan sirri da aka tattara sun nuna cewa harin bama-baman ya lalata wani muhimmin wuri a yankin Kolleram, wanda ya kasance cibiyar ayyukan sarrafa abinci na 'yan ta'adda, ciki har da injinan nika.

Kara karanta wannan

Zamfara: Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'adda 12 a wani sabon hari

"Nasarar wadannan hare-hare ta sama na kara jaddada kudurin NAF na kawar da ta'addanci da kuma tabbatar da tsaron rayukan 'yan Najeriya."

- AVM Gabkwet.

Mai magana da yawun sojojin ya ƙara da cewa za a ci gaba da kai ire-iren waɗannan hare-hare da nufin kakkaɓe duk wani nau'in ta'addanci a Najeriya, Punch ta ruwaito.

Sojojin sun kashe mutane a Yobe

A wani rahoton kuma, an ji zanga-zanga ta ɓarke a Gashua da ke jihar Yobe yayin da ake zargin dakarun sojoji sun kashe mutane akalla hudu.

Ganau ya bayyana cewa sojojin sun buɗe wa mutane wuta a shingen binciken su da ke Tashan Kuka, lamarin da ya fusata mazauna yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel