Yan Ta’adda Sun Halaka Sojoji da Dama a Wani Mummunan Kwanton Bauna

Yan Ta’adda Sun Halaka Sojoji da Dama a Wani Mummunan Kwanton Bauna

  • Rahotanni sun nuna cewa akalla sojoji shida ne aka kashe a wani harin kwanton bauna da 'yan bindiga suka shirya masu a jihar Neja
  • Hedikwatar sojoji a ranar Lahadi ta sanar da cewa 'yan bindigar sun farmaki sojojin ne a kauyen Karaga da ke Shiroro yayin rangadi
  • Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce tuni aka yi jana’izar Musulmai daga cikin sojojin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hedikwatar sojojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami’anta shida a wani harin kwantan bauna da aka kai masu a kauyen Karaga da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe mutane 3 a Zamfara, fusatattun matasa sun yi zanga-zanga

Hedikwatar sojoji ta yi magana kan sojoji shida da aka kashe a jihar Neja
Rundunar sojojin ta ce tuni aka yi jana’izar Musulmai daga cikin sojojin da aka kashe. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

"Sun fafata da 'yan ta'addan" - Nwachukwu

An kashe sojojin shida daga shiyya ta daya ta sojojin da aka tura a Allawa da Erena, a yayin da suka fita wani wani sintiri na yaki a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai sun fafata da 'yan ta'addan kuma sun kashe da dama daga cikinsu tare da jikkata wasu kafin suka amsa kiran mahaliccin su.

Hedikwatar sojojin ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter inda ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 19 ga watan Afrilu, 2024.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce tuni hukumomin sojin kasar suka tuntubi iyalan jami'an da suka mutu domin sanar da su.

"An yi jana'izar sojoji Musulmai" - Nwachukwu

Nwachukwu ya kuma ce an yi jana’izar wadanda suka kasance Musulmai daga cikin sojojin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, bisa sahalewar iyalansu.

Kara karanta wannan

Neja: An shiga fargaba bayan 'yan bindiga sun sake hallaka sojoji tare da sace Kyaftin

Sanarwar da Nwachukwu ya fitar ta kara da cewa:

"Babban hafsan sojojoji ya samu wakilcin Manjo Janar Kelvin Aligbe (TRADOC) a wajen jana'izar sojojin da aka yi a makabartar sojoji ta Minna.

Nwachukwu ya kuma bukaci al’ummar jihar Neja da su ci gaba da ayyukansu na yau da kullum, ya na mai basu tabbacin cewa sojoji da sauran jami’an tsaro za su tabbatar da tsaron su a kowane lokaci.

'Yan bindiga sun kai hari Zamfara

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gungun 'yan bindiga sun kai hari kauyen Tsafe da ke jihar Neja inda aka kashe fararen hula uku tare da jikkata wasu mutanen da dama.

Harin wanda 'yan bindigar suka kai a yau Lahadi, an rahoto cewa harsasan bindiga ne ya sami fararen hular yayin artabun da sojoji suka yi da 'yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel