Dakarun Soji Sun Dakile Harin Yan Bindiga, Sun Sheke 7 a Jihar Zamfara

Dakarun Soji Sun Dakile Harin Yan Bindiga, Sun Sheke 7 a Jihar Zamfara

  • Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu yayin da suka yi yunkurin kai hari kan sansanin sojoji a jihar Zamfara
  • Dakarun sojin Operation Hadarin Daji sun daƙile harin tare da sheke yan bindiga 7, wasu da dama sun gudu ɗauke da raunuka
  • Kwamandan rundunar sojin, Manjo Janar Godwin Mutkut ya yaba wa dakarun bisa wannan nasara da suka samu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Zamfara - Rundunar sojin Operation Hadarin Daji ta daƙile yunkurin yan bindiga na kai hari kan tawagar sojoji ranar Litinin, 24 ga watan Yuli, 2023 a jihar Zamfara.

Yayin daƙile harin, sojojin sun sheƙe yan bindiga Bakwai a musayar wuta a Kango Sabuwal, ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

Jami'an rundunar sojin Najeriya.
Dakarun Soji Sun Dakile Harin Yan Bindiga, Sun Sheke 7 a Jihar Zamfara Hoto: channelstv
Asali: Twitter

Dakarun rundunar sashi na 1 tare da sojojin da aka girke a Wanke ne suka ɗana harin kwantan bauna akan hanyar da ake zargin ‘yan bindiga ne ke amfani da ita.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Mutane Sama da 100 Kan Zargin Aika Muggan Laifuka Daban-Daban a Arewa

Wata majiyar soji, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Channels tv cewa sojojin sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga a kalla bakwai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika majiyar ta ƙara da cewa sojojin sun kuma jikkata wasu yan bindiga da dama, waɗanda suka ari na kare ɗauke da raunukan harbin bindiga.

Ya ce jim kaɗan bayan gumurzu da maharan, jami'an sojin ba su tsaya nan ba suka bi sawun yan bindigan da suka gudu domin tsira da rayuwarsu, suka kwato makamai da Babura 6.

An yaba wa sojojin da suka samu wannan nasara

Kwamandan rundunar sojin Operation Hadarin Daji da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Arewa maso yamma, Manjo Janar Godwin Mutkutx, ya yaba wa dakarun sojin bisa ƙwazon da suka yi.

Kwamandan ya jinjina wa sojojin bisa jajircewa, kwarewa da gwarzontakar da suka nuna wa yan bindigan har suka samu galaba a kansu.

Kara karanta wannan

‘Yan Sandan Nasarawa Sun Bi Motar Da Aka Sace Daga Jihar Zuwa Taraba, Sun Kamo Mutane Biyu

Zamfara na ɗaya daga jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya, waɗanda hare-haren yan bindiga ya hana al'umma zaman lafiya.

Yan Daba Sun Banka Wa Ofishin Kamfen Dan Takarar Gwamna a Jihar Kogi

A wani rahoton na daban Yan bindiga da ake zaton yan daban siyasa ne sun ƙona ofishin kamfen jam'iyyar SDP da ke Lokoja, jihar Kogi.

Daga cikin abubuwan da maharan suka lalata yayin wannan hari har da kayayyaki masu daraja da takardu. An kuma kona motocin da ke cikin ofishin yakin neman zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel