Mahara Sun Farmaki Dalibai Mata a Jami’ar Tarayya da Ke Arewa, Sun Tafka Barna

Mahara Sun Farmaki Dalibai Mata a Jami’ar Tarayya da Ke Arewa, Sun Tafka Barna

  • An shiga jimami bayan wasu mahara sun farmaki dalibai a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Lokaja a jihar Kogi
  • Maharan wadanda ake zargin ‘yan fashi ne sun kai harin ne dakin kwanan dalibai mata inda suka ji wa wasu dalibai biyu rauni
  • Wata da abin ya faru da ita ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce maharan sun shafe awa biyu su na fashin a dakunansu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Wasu mahara da ake zargin ‘yan fashi ne sun farmaki dakin kwanan dalibai a Jami'ar Tarayya da ke jihar Kogi a birnin Lokoja.

Maharan sun kai harin ne a dakin kwanan da ke wajen makarantar inda suka raunata dalibai guda biyu.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an tsaro da bincike 5 da aka taɓa tuhuma kan saɓa doka

Yan fashi sun kai hari dakin kwanan dalibai, sun raunata guda wasu da dama
Yan fashin sun sace wayoyi da kudi a dakin kwanan dalibai a jihar Kogi. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Barnar da 'yan fashin suka yi

‘Yan fashin sun farmaki daliban da misalin karfe uku na dare inda suka tafka musu barna da kuma yi musu barazana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin harin, ‘yan fashin sun kwace wayoyi da kudi da sarkoki da sauran kayayyaki masu matukar amfani, cewar Daily Trust.

Wata daga cikin wadanda abin da ya shafa, Funke Adewoye ta ce maharan sun farmaki dakunan nasu ne inda suka shafe fiye da awa biyu.

“Miyagun da suka kai wannan hari suna da yawa, sun raba kawunansu kashi uku inda suka rabu zuwa dakunan kwanan dalibai.”
“Sun ci zarafinmu da kuma yi mana barazana, sun daka mu, sun kwashe mana kayayyaki yayin da wasu dalibai suka samu munanan raunuka.”
“Dalibai daga ciki sun samu munanan raunuka a hannunsu da kuma bayansu saboda sun ki ba da wayoyinsu da kudi a kan lokaci.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutane suna tsaka da Sallar Asham a watan Ramadana a Katsina

- Funke Adewoye

An tafka asarar rayuka a hatsarin mota

Har ila yau, a jihar Kwara, mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Iyemoja a ƙaramar hukumar Moro ta jihar Kwara.

Rahotanni sun tabbatar cewa hatsarin wanda ya auku da misalin ƙarfe 06:40 na safe ya ritsa da motoci biyu, wata babbar motar ƙirar Volvo da wata motar bas.

Yan bindiga sun hallaka jami’an CPG

Kun ji cewa wasu mahara sun farmaki jami’an tsaron CPG da ke jihar Zamfara inda suka tafka musu barna.

Yayin harin maharan sun hallaka jami’an CPG tare da kona motar jami’an tsaro a karamar hukumar Tsare sa ke jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel