Dalibar Aji 4 a Jami’ar Najeriya Ta Dauki Ranta da Kanta, an Gano Dalili

Dalibar Aji 4 a Jami’ar Najeriya Ta Dauki Ranta da Kanta, an Gano Dalili

  • Rahotanni sun bayyana cewa wata dalibar jami'ar jihar Kwara ta sha maganin kwari wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta
  • Dalibar mai suna Rashidat Shittu ta dauki ranta da kanta ne a saboda samun matsala da take yi a karatunta
  • An gano cewa ‘yan uwa da ma’aikatan jami'ar KWASU ne suka binne marigayiyar a a makabartar Musulmai ta Osere, Ilorin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kwara - Wata dalibar aji hudu a jami’ar jihar Kwara, Malete da ke karamar hukumar Moro, mai suna Rashidat Shittu, ta dauki ranta da kanta saboda ta samu matsala a karatunta.

A cewar abokan karatunta da suka bayyana wa jaridar Sunday PUNCH, marigayiyar ta dauki ranta ne gabanin jarrabawar da ta ke tafe ta hanyar shan maganin kwari.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

Dalibar jami'ar Kwara ta dauki ranta da kanta
Wata dalibar jami'ar Kwara ta bakunci lahira bayan ta sha maganin kashe kwari. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

An sanar da mutuwar Shittu a lokacin da aka kaita asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin domin ceto rayuwarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Leadership ta tattaro cewa an fara kai ta asibitin makaranta kafin daga bisani a kai ta asibitin koyarwar domin ceto rayuwarta.

Rashidat Shittu ta dauki ranta saboda matsalar karatu

Har ila yau, wata ma’aikaciyar da ke cikin tawagar likitocin da suka duba lafiyarta a UITH amma ta nemi a sakaya sunanta ta ce an kawo dalibar ne a mace.

Ta ce:

“Abokan karatunta sun ce tana fama da damuwa ne saboda sakamakon karatunta ba shi da kyau, a ranar kuma ta fada masu tana jin radadi a jikinta saboda ta sha maganin kwari."

An gano cewa ‘yan uwa da ma’aikatan sashen kula da harkokin dalibai na KWASU ne suka binne marigayiyar a a makabartar Musulmai ta Osere, Ilorin.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

Sai dai da aka tuntubi daraktar hulda da jami’ar KWASU, Dokta Saeedat Aliyu, a cikin sakon da ta aike ta wayar tarho, ta ce ba ta da labarin rasuwar dalibar.

Dalibar kwaleji ta dauki ranta saboda saurayi

A wani labarin da Legit Hausa ta ruwaito a baya, wata daliba ta sha maganin kashe kwari ta mutu saboda saurayinta ya nemi su kawo karshen soyayyar su.

Jamima Shetima Balami, dalibar ND II ce a sashen koyon aikin jarida a kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Mubi a jihar Adamawa.

Rahotanni sun bayyana cewa Jamima ta dauki ranta ne bayan da wani saurayinta da ake kyautata zaton malamin jami'a ne ya nemi su kawo karshen soyayyar da suke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel