'Yan Bindiga Sun Kai Ƙazamin Hari Hedkwatar Ƙaramar Hukuma, Sun Kashe Jami'an Tsaro a Arewa

'Yan Bindiga Sun Kai Ƙazamin Hari Hedkwatar Ƙaramar Hukuma, Sun Kashe Jami'an Tsaro a Arewa

  • Ƴan bindiga sun kai hari hedkwatar ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, sun kashe dakaru 2 na rundunar ƴan sa'kai CPG
  • Wani mazaunin garin ya bayyana cewa maharan sun yi yunƙurin sace ɗaliban kwalejin horar da malaman lafiya ta Tsafe amma ba su cimma nasara ba
  • Ya ce ƴan bindiga sun ƙona motoci biyu na jami'an tsaro amma bisa tilas suka gudu ɗauke da raunukan harbin bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Wasu gungun ƴan bindiga sun sake kai kazamin hari garin Tsafe, hedkwatar ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro, ƴan bindiga sun kashe jami'an rundunar ƴan sa-kai (CPG) tare da ƙone motoci biyu na rundunar sojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari ana shirin shan ruwa, sun tafka ɓarna tare da sace matan aure a Arewa

Sojojin Najeriya.
Jami'an CPG sun mutu a harin ƴan bindiga Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Wani mazaunin garin, Malam Usman Tsafe, ya shaidawa ƴan jarida ta wayar tarho cewa ƴan bindigar sun kewaye garin ɗauke da muggan makamai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, da farko ƴan bindigar sun raba kansu zuwa gida uku, inda tawagar farko ta yi yunkurin kai farmaki kwalejin horar da malaman lafiya da fasaha da ke garin.

Sauran kaso biyun kuma suka kutsa kai cikin garin, sannan suka buɗe wuta domin su tsorata jama'a kuma su samu saukin sace mutane da ɗaliban makaranta.

Jami'an tsaro sun fafata da maharan

Ya ƙara da cewa ɗaukin da jami'an tsaro suka kawo a kan loƙaci, shi ne ya sa maharan suka ja da baya, suka arce zuwa cikin jeji bayan musayar wuta.

"Yayin murayar wuta da ƴan ta'addan, jami'an rundunar CPG biyu suka rasa rayuwarsu yayin ƴan bindiga suka ƙone motocin sintiri biyu na sojojin Najeriya da CPG ta Zamfara," in ji shi.

Kara karanta wannan

Bauchi: Adadin mutanen da suka mutu a wurin rabon zakkah ya ƙaru, an faɗi sunayensu

Mutumin ya ce ƴan bindigan ba su iya jurewa musayar wuta da jami'an tsaron ba, bisa tilas suka gudu ɗauke da raunukan harbin bindiga, rahoton Daily Trust.

Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da yawan hare-haren ƴan bindiga na garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kashe-kashe.

Sheikh Gumi ya shiga matsala

A wani rahoton kuma Ƙungiyar RUN ta caccaki fitaccen malamin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi bisa zarginsa da alaƙa da ƴan bindiga.

RUN ya bukaci hukumomin tsaron Najeriya da su maida hankali kan Sheikh Gumi, kuma ta sanya shi cikin waɗanda take nema ruwa a jallo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel