Jerin Manyan Jami'an Tsaro da Bincike 5 da Aka Taɓa Tuhuma Kan Saɓa Doka

Jerin Manyan Jami'an Tsaro da Bincike 5 da Aka Taɓa Tuhuma Kan Saɓa Doka

Kowane jami'in tsaro da na bincike da aka dauka aiki ya kan ɗauki rantsuwa domin kare dukiyoyi da rayukan al'umma.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Amma wasu daga ciki su na komawa satar dukiyoyin jama'a ko kuma aikata ayyuka da suka saba doka idan suka samu dama.

Manyan jami'an tsaro 5 da aka zarga da aikata manyan laifuffuka
Jami'an tsaron an zarge su da saba dokokin Najeriya. Hoto: Abba Kyari, Sambo Dasuki, Abdulrashid.
Asali: Facebook

Har ila yau, wasu su na amfani da damar da suka samu domin hada baki da wasu bata gari domin karya dokar kasa da suka yi rantsuwa a kanta.

Legit Hausa ta jero muku wasu daga cikin jami'an tsaro da ake zarginsu da saɓa dokar ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Mahara sun farmaki dalibai mata a Jami'ar Tarayya da ke Arewa, sun tafka barna

1. Tafa Balogun

Tsohon Sufetan 'yan sandan ya rasu a watan Agustan 2022 kafin ya yi ritayar dole saboda badakalar kudi a 2005.

Balogun ya rasa girmansa bayan karamin dan sanda kuma shugaban Hukumar EFCC a wancan lokaci, Nuhu Ribadu ya kama shi dumu-dumu, cewar The Nation.

2. Abba Kyari

Kyari wanda mataimakin kwamishinan 'yan sanda ne ya yi kaurin suna a rundunar kafin zarginsa da hada kai da ɗan damfara Ramon Abbas da aka fi sani da 'Hushpuppi', cewar Premium Times.

Har ila yau, an zargi Kyari da harkar kwaya wanda ya tayar da ƙura a kasar inda wasu ke mamakin yadda jarumin dan sandan zai aikata irin wannan kuskure.

3. Abdulrashid Bawa

Abdulrashid Bawa ya riƙe shugabancin hukumar EFCC kafin Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi tare da fara bincike a kansa.

Ana zargin Bawa da hada kai da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele wurin almundahana da dukiyar ƙasa, cewar BBC Pidgin.

Kara karanta wannan

Akwai hannun na kusa da Buhari: Omokri ya fallasa wadanda suka kubutar da wakilin Binance

4. Sambo Dasuki

Tsohon sojan ya rike mukamin mai ba da shawara ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan kan harkokin tsaro.

A shekarar 2015, hukumar tsaro ta DSS ta cafke Sambo Dasuki kan zargin karkatar da kudin makamai domin yaki da ta'addanci a Najeriya.

5. Abdullahi Dikko Inde

A shekarar 2016, hukumar EFCC ta cafke tsohon shugaban hukumar Kwastam, Abdullahi Dikko Inde kan zargin badakalar N40bn, cewar BusinessDay.

Bayan kudin shiga daga bangaren haraji da kuma man fetur, hukumar Kwastam ita ce ta uku wurin kawo kudin shiga ga Najeriya.

Abubuwa 10 masu muhimmanci ga mai azumi

Kun ji cewa akwai wasu muhimman abubuwa da ya kamata mai azumi ya ba su kulawa na musamman a wannan wata.

Sannan akwai wasu abubuwa da ya kamata Musulmi ya tabbatar ya guje su musamman a wannan wata mai albarka na Ramadan.

Wannan rahoto zai kawo muku su tare da yin bayani ga kowannensu domin rabauta a wannan wata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel